Gwamnatin Buhari ta bada sharadin janye dakatarwar da ta yi wa kamfanin Twitter

Gwamnatin Buhari ta bada sharadin janye dakatarwar da ta yi wa kamfanin Twitter

- Gwamnatin Tarayya ta ce za a iya janye dakatarwar da aka yi wa Twitter

- Ministan harkokin waje ya zauna da Jakadun kasar waje dazun nan a Abuja

- Geoffrey Onyeama yace za a koma morar Twitter idan kamfanin ya bi doka

Gwamnatin Tarayya ta fara magana game da dakatarwar da ta yi wa kamfanin Twitter, aka hana su aiki a Najeriya.

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 7 ga watan Yuni, 2021, cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta fara magana a kan lamarin.

Ministan harkokin kasar waje, Geoffrey Onyeama, ya bayyana cewa Twitter zai dawo aiki a Najeriya idan har kamfanin zai bi dokokin Najeriya.

KU KARANTA: Twitter ta tanka Gwamnatin Najeriya bayan ta dakatar da ita

Da yake magana da wasu jakadan kasar waje, Geoffrey Onyeama yace, za a cigaba da amfani da Twitter yadda aka saba idan kamfanin ya yi abin da ya dace.

Da aka jefawa Ministan harkokin wajen tambaya game da lokacin da mutanen Najeriya za su iya cigaba da hawa dandalin Twitter, sai ya ce babu rana.

Onyeama ya ce: “Babu wani kaiyadajajjen lokaci game da wannan, amma sharadin shi ne ayi abin da ya kamata wajen amfani da shafukan sada zumunta.”

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Geoffrey Onyeama, ya tabbatar da cewa ya zama dole a bi ka’ida.

KU KARANTA: Hana Twitter: An take dokar kasa, an yi wa tsarin mulki karon tsaye - Chinda

Gwamnatin Buhari ta bada sharadin janye dakatarwar da ta yi wa kamfanin Twitter
Geoffrey Onyeama Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Ba mu cewa Twitter na yi wa kasar nan barazana ko wani abu irin haka; abin da ya sa mu ka yi wannan shi ne mu hana ayi amfani da su wajen tada fitina.”

Ministan ya ce gwamnatin tarayya ba za ta zura idanu ayi amfani da kafar Twitter wajen tada zaune-tsaye, ko miyagu su nemi su rika tada kafar baya.

Kafin yanzu jaridar The Nation ta ce za ayi zama na musamman tsakanin bangaren gwamnatin tarayya da wasu jakadan kasar waje a safiyar ranar Litinin.

Dazu kun ji labari cewa kan kwararru ya hadu a kan cewa an yi kuskure wajen hana amfani da Twitter, su ka ce an ba gwamnatin tarayya shawarar banza.

A na su ra'ayin, haramta yin Twitter zai kara yawan masu zaman banza, ya kora masu hannun jari domin ana amfani da shafin wajen yin talla ta yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng