'Yan Bindiga Sun Sace Shanu 500 a Garuruwan Jihar Kebbi

'Yan Bindiga Sun Sace Shanu 500 a Garuruwan Jihar Kebbi

- Yan bindiga sun kai hari wasu garuruwa a karamar hukumar Sakaba na jihar Kebbi

- Yan bindigan da suka shiga garin kan babura sun sace kimanin shanu 500 a cewar shugaban yan banga

- Ba a rasa rai ba yayin harin na yan bindigan domin shanu kawai suka zo

Yan bindiga, a ranar Lahadi, sun sace shanu 5000 a garuruwa daban-daban a karamar hukumar Sakaba a jihar Kebbi, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar yan sakai na masarautar Zuru, John Mani, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin magana da majiyar Legit.ng a hirar wayar tarho.

'Yan Bindiga Sun Sace Shanu 500 a Garuruwan Jihar Kebbi
'Yan Bindiga Sun Sace Shanu 500 a Garuruwan Jihar Kebbi. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Hukumar Yan Sanda Ta Dakatar Da Bada Izinin Amfani Da Gilashin Mota Mai Duhu

Ya ce hatsabiban yan bindigan sun dade suna adabar mutanen masarautar a cikin yan makonnin baya bayan nan.

Sakaba na daya daga cikin kananan hukumomi hudu da ke masarautar Zuru a jihar ta Kebbi.

A ranar alhamis da ta gabata, yan bindiga sun halaka mutane 88 a kauyuka takwas a kananan hukumomin Danko/Wasagu.

A cewarsa, yan bindigan da suka saba kutsawa garin ta cikin jihohin Kebbi/Zamfara da iyakokin Kebbi/Niger sun kai hari a garuruwan da tsakar rana sun sace shanu da dama.

Mani ya ce babu wanda ya rasa ransa a garin sakamakon harin yan bindigan da suka zo da babura kimanin 500, kowanne dauke da fasinja daya ko biyu.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Buhari Ya Naɗa Wa Mai Ɗakinsa, Aisha, Sabbin Hadimai Biyu

Ya ce, "Yan bindiga daga Zamfara da Niger sun kai hari wasu garuruwa a karamar hukumar Sakaba na jihar Kebbi sun sace shanu a ruga biyar.

"A kowanne ruga, akwai a kalla shanu 500. Ba su kashe kowa ba duba da cewa shanu kawai suka zo sata."

Mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar, bai dauka wayarsa ba da wakilin majiyar Legit.ng ya kira shi domin jin ba'asi.

Bai kuma amnsa sakon kar ta kwana da aka aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'

Asali: Legit.ng

Online view pixel