Tsohon Shugaban INEC, Attahiru Jega ya fadi babban abin da ya hana Najeriya cigaba
- Farfesa Attahiru Jega ya yi jawabi a wajen laccar tunawa da Lateef Jakande
- Tsohon Shugaban hukumar INEC ya yi tir da irin Shugabannin da ake da su
- Jega ya yabi tsohon Gwamna Jakande, ya ce ba za a taba mantawa da shi ba
Tsohon shugaban hukumar zabe na kasa watau INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya ce Najeriya ta tara jagorori masu son-kai, marasa kishin kasa da hangen nesa.
Jaridar Daily Trust ta ce Attahiru Jega ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar, 5 ga watan Yuni, a wajen laccar da aka shirya domin tunawa da Lateef Jakande.
Farfesa Attahiru Jega yana cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a wajen wannan lacca na musamman da kungiyar Federal Social Democrats ta shirya.
KU KARANTA: Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Lateef Jakande
Attahiru Jega ya halarci taron ne ta yanar gizo, ya ce rashin shugabannin masu hangen nesa ya jawo kasar nan ta gagara cigaba sosai kamar yadda ya kamata.
“Dole ne da farko mu yarda Najeriya ta gamu da masifar samun wasu tarkace rike da shugabanci, masu kwadayi da rashin hangen nesa, wadanda ba su da komai sai hadama, ba su san sha’anin mulki ba, sannan suna ganganci wajen gudanar da shugabanci.” Inji Jega.
Kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto a dazu, Farfesan sha’anin harkar siyasar ya ce shugabannin da ake da su, sun ci moriyar tabarbarewar da siyasar Najeriya ta yi.
“Daga cikin kalubalen da ake fuskanta a siyasar Najeriya, shi ne akwai shugbanni marasa kishi, masu son-kai, da za su ciyar da kasar gaba da fuskar siyasar tattalin arziki domin a kai ga ci.”
KU KARANTA: Bayan rage kudin makaranta, Gwamnan Oyo zai karawa 'Yan NYSC alawus
Jega wanda ya rike shugaban hukumar INEC ya cigaba: “Kafin abubuwa su dawo daidai, dole sai an samu shugabanni marasa son-kai, da su ke da hangen nesa.”
A jawabinsa, Farfesa Jega ya ce Marigayi Lateef Jakande shugaba ne wanda bai da kwadayi. “Shugaba ne mai hangen nesa wanda ya taba rayuwar jama’a.”
“Za a iya cewa ya taba rayuwar mutane da yawa, ya dage a wajen dabbaka manufofinsa, har abada ba za a taba mantawa da abubuwan da ya yi ba.” Inji Attahiru Jega.
A farkon shekarar nan ne Lateef Jakande ya rasu, har sai da shugaba Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar gwamnan farko na farar hula da aka yi a jihar Legas.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana Lateef Jakande wanda ya rasu ya na shekara 91 a matsayin wanda yayi rayuwa domin jin dadin wasu ba karon kansa ba.
Asali: Legit.ng