An ba Shugaban Hukumar NITDA Isa Pantami lambar yabo

An ba Shugaban Hukumar NITDA Isa Pantami lambar yabo

- Shugaban NITDA ya samu lambar yabo na musamman a 2018

- ‘Yan jaridun kasar ne su ka ba Isa Pantami kyauta kwanan nan

- Manema labarai sun ce Shugaban NITDA ne abokin su na bana

Mun samu labari cewa ‘Yan Jaridar Najeriya karkashin Kungiyar nan ta NUJ ta ba Shugaban Hukumar NITDA watau Sheikh Dr. Isa Ibrahim Ali Pantami lambar yabo a makon da ya wuce.

An ba Shugaban Hukumar NITDA Isa Pantami lambar yabo
'Yan jarida sun ba Shugaban NITDA lambar yabo na 2018

‘Yan Jaridar kasar nan da ke lemar NUJ ta ba Shugaban Hukumar da ke kula da cigaban ilmin yada bayanai ta na’urorin zamani na NITDA watau Isa Ali Ibrahim Pantami kyauta na zama Jami’in Gwamnatin da ya fi kowane shiri da ‘Yan jarida.

KU KARANTA: Abdussalami yace dole a kawo karshen kashe-kashen hauka a Najeriya

Kungiyar NUJ ta kasar ta ce Shugaban Hukumar ta NITDA Isa Pantami ya fi kowa faram-faram da manema labarai a cikin masu rike da Hukumomi da Ma’aikatu a Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a wannan shekarar da ake ciki.

Wani daga cikin Hadiman Shugaban Kasar mai suna Bashir Ahmaad wanda na-kusa da Shugaban na NITDA ne ya bayyana cewa Shehin Malamin ya cancanci wannan lambar yabo don kuwa ba ga ‘Yan jarida ba kurum, Malamin abokin kowa ne.

Shugaban Kungiyar 'Yan jaridar kasar Abdulwahid Odusile da kuma Sakataren sa Shuaibu Usman Leman su ka sa hannu a wannan kyauta. Ba dai yau aka saba jinjinawa aikin Dr. Isa Pantami ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel