Karen bana: ‘Yan Najeriya sun fito da satar amsar fasahar da za ta sa a cigaba da yin Twitter a asirce

Karen bana: ‘Yan Najeriya sun fito da satar amsar fasahar da za ta sa a cigaba da yin Twitter a asirce

- An soma neman yadda za a kewaye haramta aiki da Twitter da aka yi a Najeriya

- Wadanda suka san dawar garin sun ce za a iya hawa Twitter idan aka samu VPN

- Daga cikin masu bada wannan shawara har da tsohon Hadimin gwamnatin Kano

Mutanen Najeriya sun zabi su rika amfani da abin da ake kira Virtual Private Networks, wanda aka fi sani da VPN domin su samu damar amfani da Twitter.

Jaridar Daily Trust ta ce an samu wadansu sun fara ba mutane shawarar yadda za su gujewa matakin da gwamnati ta dauka na haramta ziyartar shafin.

Mutane da-dama sun nuna ba su ji dadin matsayar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauka na hana aiki da dandalin sada zumuntan zamanin ba.

KU KARANTA: Gwamna ya rage albashin Ma'ikata da alawus

An tsakuro kadan daga cikin abubuwan da wasu ke fada a shafin na Twitter:

“Za ka iya yin Twiter idan ka na so, idan kana amfani da VPN, gwamnati ba za ta iya yin komai ba. Da #TwitterBanInNigeria (aka haramta Twitter), hakan yana nufin babu jami’in gwamnati da zai yi mana jawabi ta nan, kuma su kansu jami’an gwamnatin bai kamata a ga suna bibiyar dandalin ba. Sune su ka yi rashi.” Inji Salihu Tanko Yakassai.

Wani mutum kuma ya rubuta:

"Za ka iya sauke manhajar VPN a wayar salularka, yayin da gwamnati ta ke toshe kafar @Twitter Najeriya."

KU KARANTA: Tunde Bakare yana ganin tsofaffin da ke kan mulki suka fara lalata Najeriya

‘Yan Najeriya sun fito da satar amsar fasahar da za ta sa a cigaba da hawa shafin Twitter a asirce
Shugaban Najeriya

"Shin Lai Mohammed ya san akwai wani kankanin abu da ake kira VPN, da ‘Yan Najeriya za su iya kewaye wa hanin da gwamnatin tarayya ta yi a kan Twitter a kasar.” Inji Farouk Kperogi, ya na kaca-kaca da gwamnatin APC.

Wata mai zama a Amurka ta rubuta:

“Ka sauke manhajar “Windscribe VPN” daga App Store, ka bude shafinka, ka zabi lambar sirri, ka bayyana wurin da ake zama. Sai ka zabi samfurin da ake amfani da manhajar kyauta. Daga nan kuma sai ka tantance akwatinka na E-mail.”

Dazu nan rahoto ya zo mana Gwamnatin Tarayya ta dakatar da hana dandalin sada zumunta a Twitter, ma'aikatar labarai da al'adu ta bada sanarwar.

Ministan sadarwa da al'adu, Lai Mohammed ya sanar da dakatarwar, ya na cewa ana amfani da shafin wurin yin abubuwa da za su iya tada zaune tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng