Hukumar FBI ta yi magana game da zargin dangantakar Dr. Isa Pantami da Boko Haram

Hukumar FBI ta yi magana game da zargin dangantakar Dr. Isa Pantami da Boko Haram

- Hukumar FBI ta yi magana game da zargin da ake yi wa Dr. Isa Ali Pantami

- FBI ta ki cewa uffan a kan alakar Ministan tarayyar da kungiyar Boko Haram

- Wata jarida ta jefi Ministan da samun dangantaka da ‘Yan ta’adda a Najeriya

Zargin da ake yi na alakanta Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin Najeriya, Dr. Isa Ali Pantami, da Boko Haram ya zagaye ko ina a Duniya.

A dalilin wani rahoton bogi da aka fitar ana alakanta Isa Ali Pantami da ‘yan ta’adda, hukumar FBI ta fito ta yi magana kamar yadda Leadership ta fada.

Jaridar ta ce FBI mai bincike a kasar Amurka ta aiko mata martani game da wannan rade-radi, ta ce amma ba za ta iya gaskata ko ta karyata zargin ba.

KU KARANTA: Abin da ya sa Sheikh Isa Pantami ya yi Muƙabala da Mohammed Yusuf

A amsar da ta ba ‘yan jarida, hukumar FBI ta ce ba za ta iya fito wa fili ta ce wane da wane su na cikin jerin mutanen da ta ke nema ruwa a jallo a Duniya ba.

“Mun gode da ku ka tuntube mu. Amma saboda yadda mu ka saba aiki, ba za mu iya tabbatar ko mu musanya wani ya na cikin mutanen da mu ke nema ba.”

Kawo yanzu dai alamu sun tabbatar da cewa babu gaskiya a jifan Ministan tarayyar da aka yi da samun wata alaka da malaman da ke hura wutar ta’addanci.

Tuni dai Dr. Isa Ali Pantami wanda ya yi karatu a kasar Saudi Arabiya da kasashen Larabawa ya musanya samun alaka ta kusa ko ta nesa da ‘Yan Boko Haram.

Hukumar FBI ta yi magana game da zargin dangantakar Dr. Isa Pantami da Boko Haram
Ministan Tarayya, Dr. Isa Pantami
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dakarun Operation Puff Adder sun ceto wasu Matafiyan da aka sace

Lauyoyin Ministan sadarwar sun yi barazanar maka wadanda su ka yi masa wannan sharri a gaban kotu, muddin ba su fito gaban Duniya sun nemi afuwarsa ba.

Mutanen da su ka san tarihin Malamin addinin tun kafin ya zama Minista sun fito sun kare shi, su ka ce ya na cikin wadanda su ka kalubalanci akidar ‘yan ta’addan.

A dalilin haka ne gidan jaridar da ta fara wallafa wannan labari maras tushe ta yi maza-maza ta bada hakuri, ta bayyana cewa lallai ta yi kuskure a rahoton na ta.

A farkon makon nan aka ji cewa Dr. Isa Ali Pantami ya yi martani kan rubutun da aka yi a kansa na cewa ya na da hannu a cikin tafiyar 'yan ta'addan Boko Haram.

Shehin Malamin ya yi ishara ga karatuttukansa na sama da shekaru 15 in da ya ke yakar munanan akidun da shugabannin Boko Haram su ka bijiro da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel