‘Yan Majalisar PDP suna barazanar shiga kotu da Gwamnatin Buhari saboda ya haramta Twitter

‘Yan Majalisar PDP suna barazanar shiga kotu da Gwamnatin Buhari saboda ya haramta Twitter

- Bangaren marasa rinjaye a Majalisa ya soki matakin dakatar da Twitter

- Kingsley Chinda ya ce hana al’umma amfani da Twitter ya sabawa doka

- Hon. Chinda ya soki umarnin da aka bada na sa ido a kan sauran kafofi

‘Yan majalisar tarayya da ke karkashin jam’iyyar PDP suna barazanar zuwa gaban Alkali da gwamnatin Najeriya a kan dakatar da hawa shafin Twitter.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa bangaren masu adawa a majalisar wakilan tarayyan kasar, sam ba su gamsu da matakin da aka dauka na haramta Twitter ba.

‘Yan hamayyar sun bayyana cewa umarnin da aka ba hukumar NBC na sa ido kan sauraron kafofin sadarwa, yunkuri ne na shigo da kudirin ‘Social Media Bill’.

KU KARANTA: Gwamnati ta dakatar da shafin Twitter

A cewar masu adawar, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na kokarin shigo da wannan kudiri ba tare da ya bi kan teburin ‘yan majalisar tarayya ba.

Shugaban marasa rinjaye a majalisa, Honarabul Kingsley Chinda, ya fitar da jawabi, ya na cewa:

“Sanarwar ma’aikatar yada labarai da al’adu ta tarayya ta kuma bada umarni ga hukumar NBC ta yi maza ta fara lura da duk wasu OTT da kafofin sada zumunta a Najeriya.”

“Kamar yadda ake tsammani, wannan sanarwa ta girgiza wadanda suka yi imani da damukaradiyya da dokar kasa a Najeriya da daukacin Duniya.” Inji Chinda.

KU KARANTA: Shehu Sani ya hadi hanyar hawa Twitter a cikin sauki

‘Yan Majalisar PDP suna barazanar shiga kotu da Gwamnatin Buhari saboda ya haramta Twitter
Shugaba Muhammadu Buhari

A cewar Kingsley Chinda, wannan mataki da gwamnatin APC ta dauka ya saba wa dokar kasa, domin bangaren zartarwa ta yi wa ‘yan majalisa kutse a cikin aikinsu.

‘Dan majalisar ya ce haramta amfani da shafin Twitter da bada umarnin sa ido a kan sauron kafofin yada labarai, ba komai ba ne face yi wa tsarin mulki hawan kawara.

Punch ta ce a jawabin da Chinda ya fitar wanda ya yi wa take da ‘Press Release on Suspension of Twitter in Nigeria’, ya nuna za su iya zuwa gaban kotu da gwamnati.

Kun ji cewa wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka a makon jiya ya girgiza mutane, ‘yan majalisar suna ganin an saba doka, sannan an yi masu katsalandan.

Tuni jagororin adawa irinsu Bukola Saraki da Atiku Abubakar suka yi martani a kan hana mutane hawa shafin na sada zumuta, suna ganin yin hakan sam bai dace ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel