Masana sun ja-kunnen Gwamnati, hana Twitter ya na da mummunan tasiri a kan tattalin arziki

Masana sun ja-kunnen Gwamnati, hana Twitter ya na da mummunan tasiri a kan tattalin arziki

- Masana sun soki matakin dakatar da amfani da dandalin Twitter a Najeriya

- Hana mutanen kasa hawa shafin zai taba wadanda suke kasuwanci a Twitter

- Kungiyar NESG ta ce haramcin yana da tasiri sosai kan tattalin arzikin kasa

Kungiyar Nigerian Economic Summit Group da wasu masana tattalin arziki sun soki matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na hana yin amfani da Twitter.

Kamar yadda jaridar Punch ta fitar da rahoto, masanan suna ganin gwamnatin tarayya ba ta yi shawara da kyau kafin zartar da wannan danyen hukunci ba.

A wata hira da aka yi da NESG, ta ce kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa za su sha wahala a dalilin matakin, hakan zai sa tattalin kasar ya sake tabarbarewa.

KU KARANTA: Facebook tayi koyi da Twitter, ta goge jawabin Shugaba Buhari

Masana irinsu kwararren Akawun nan, Dr, Sam Nzekwe, da Farfesan tattalin arziki da tsare-tsare, Akpan Ekpo, da kuma Eze Onyekpere sun yi tir da wannan matsaya.

A cewar wadannan kwararru, dakatar da amfani da Twitter zai sa dinbin mutane su rasa aikin yi domin ana amfani da dandalin wajen yin kasuwancin yanar gizo.

‘Yan kungiyar NESG da suka yi magana da jaridar sun ce haramta aiki da Twitter zai sa masu zuba hannun jari su yi shakkar shigowa Najeriya, su yi kasuwanci.

Shugaban NESC, Laoye Jaiyeola, yake cewa Twitter sun yi kuskuren goge maganar shugaba Muhammadu Buhari, amma ya kamata ya sake duba matakin da ya dauka.

KU KARANTA: Twitter ta yi martani bayan an dakatar da ayyukanta a Najeriya

Masana sun ja-kunnen Gwamnati, hana Twitter ya na da mummunan tasiri a kan tattalin arziki
An hana yin Twitter Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Haramcin zai jawo a rasa aiki, a kara jawo matsalar rashin aikin yi. Muna rokon gwamnati ta sake duba batun. Hana Twitter bai dace ba, ba a bada shawarar kwarai ba.”

Femi Egbesola wanda shi ne shugaban kananan ‘yan kasuwa na kasa ya ce haramcin zai taba kananan ‘yan kasuwa, wanda sune 70% na masu kasuwanci a kasar.

Farfesan tattali a jami’ar Uyo, jihar Akwa Ibom, Akpan Ekpo, ya ce ba ayi tunani ba, domin hakan zai tsoratar da wadanda suke shirin zuwa Najeriya, su zuba hannun jari.

Dazu kun ji cewa ‘Yan majalisar tarayya da ke karkashin jam’iyyar PDP suna barazanar zuwa gaban Alkali da gwamnatin Najeriya a kan dakatar da hawa shafin Twitter.

Shugaban marasa rinjaye a majalisa, Honarabul Kingsley Chinda, ya fitar da jawabi a ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel