Alhaji Lateef Jakande ya yi rayuwa da jin dadin jama'a ba kansa ba, Buhari yayi alhinin mutuwarsa

Alhaji Lateef Jakande ya yi rayuwa da jin dadin jama'a ba kansa ba, Buhari yayi alhinin mutuwarsa

- Shugaba Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan tsohon gwamnan jihar

- Alhaji Jakande ya mulki Legas kafin Buhari ya cire shi bayan juyin mulkin 1979

- Jam'iyyar PDD da Atiku sun yabawa marigayin bisa ayyukan da yayi

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar gwamnan farko na farin hula na jihar Legas, Alhaji Lateef Jakande, ya siffantashi matsayin wanda yayi rayuwa don jin dadin wasu ba kansa ba.

Mai magana da yawun Buhari Femi Adesina, ya bayyana cewa Buhari ya yi rayuwa mai albarka mai cike da darrusa.

Buhari yayin jajantawa iyalansa marigayin, ya ce tsohon gwamnan ya kafa tarihin aikin alheri ga al'ummar jihar Legas.

Shugaban kasan ya ambaci irin ayyukan kwarai da yayi a matsayi gwamna kuma matsayin Ministan ayyukan wanda suka taimakawa demokradiyya a Najeriya.

A cewarsa, ya bar darussan da za'a cigaba da daukan hikima daga gresu na tsawon shekara da shekaru musamman wajen sanya jin dadin mutane a gabansa.

DUBA NAN: Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da marigayi Alhaji Lateef Jakande

Alhaji Lateef Jakande ya yi rayuwa da jin dadin jama'a ba kansa ba, Buhari yayi alhinin mutuwarsa
Alhaji Lateef Jakande ya yi rayuwa da jin dadin jama'a ba kansa ba, Buhari yayi alhinin mutuwarsa Credit: Presidency
Asali: Facebook

DUBA NAN: Majalisar Dattawa ta gayyaci Gwamnan CBN yayi bayani kan haramta Bitcoin

Alhaji Jakande ya rasu ne yana da shekaru 91.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da hakan a shafinsa na Tuwita ranar Alhamis.

"Ina mai sanar da mutuwar mutumin kirki, babban dan siyasa, kuma gwamnan jihar Legas na farko, Alhaji Lateef Kayode Jakande," Sanwo Olu yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel