Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da marigayi Alhaji Lateef Jakande
Gwamnan jihar Legas na farin hulan na farko, Alhaji Lateef Jakande, ya rigamu gidan gaskiya da safiyar Alhamis, 11 ga watan Febrairu, 2021.
Ga jerin abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da marigayin dattijon:
1. An haifi Alhaji Lateef Jakande ranar 23 ga Yuli 1929, kuma ya shahara da sunan Baba Kekere.
2. A bisa bayanin da gwamnatin jihar Legas tayi, iyayen marigayin sun zo ne daga garin Omu-Aran a jihar Kwara.
3. Ya yi aiki a gidan jaridar Nigerian Tribune, inda ya zama Cif Edita
4. Tsohon shugaban yankin Yarabawa, Obafemi Awolowo ne ya shawarceshi yayi takaran kujeran gwamnan Legas a 1979 kuma ya lashe zaben karkashin jam'iyyar Unity Party of Nigeria.
5. An cireshi daga mulki ne lokacin juyin mulkin da shugaba Muhammadu Buhari yayi a Disamban, 1983.
DUBA NAN: Zama da ‘Yan bindiga ne hanyar kawo zaman lafiya – Matawalle ya fadawa Gwamnoni
KU KARANTA: Rashin tsaro: mun gaza sauke nauyin da aka daura mana, in ji Kakaki
6. Tarihi ya nuna cewa Alhaji Jakande ya yi rayuwa cikin tawali'i inda yayi rayuwar cikin gidan kansa ba na gwamnati ba kuma da motar kansa yake zuwa aiki.
7. Bayan juyin mulkin 1983, an damke Jakande kuma aka yanke masa hukuncin shekaru 7 a kurkuku. Daga baya aka sake shi.
8. Kadan daga cikin abubuwa zo a gani da yayi sune kafa jami'ar jihar Legas, makarantun firamare da sakandare kyauta, gine-gine gidaje ga mutane, kwale-kwalen haya da sauransu.
9. Marigayin ne mu'assasin kwaljen ilmin aikin jaridar NIJ a 1963 kuma wanda ya bada shawaran kafa kungiyar masu kamfanonin jarida da kuma kungiyar Editoci a Najeriya.
10. Ana ikirarin cewa babu dan siyasa irinsa yanzu a Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar gwamnan farko na farin hula na jihar Legas, Alhaji Lateef Jakande, ya siffantashi matsayin wanda yayi rayuwa don jin dadin wasu ba kansa ba.
Mai magana da yawun Buhari Femi Adesina, ya bayyana cewa Buhari ya yi rayuwa mai albarka mai cike da darrusa.
Buhari yayin jajantawa iyalansa marigayin, ya ce tsohon gwamnan ya kafa tarihin aikin alheri ga al'ummar jihar Legas
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng