Ana kiran soke NYSC, Gwamna ya yi alkawarin karawa duk ‘Dan bautar kasar jiharsa alawus

Ana kiran soke NYSC, Gwamna ya yi alkawarin karawa duk ‘Dan bautar kasar jiharsa alawus

- Gwamnatin Seyi Makinde za ta kara alawus din da ake biyan ‘Yan hidimar kasa

- Gwamnan ya bayyana wannan yayin da ya ziyarci sansanin NYSC na jihar Oyo

- Makinde ya ba matasan da ke wannan aiki a jiharsa labarin aurensa da sahibarsa

Mun samu labari cewa Mai girma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya sha alwashin kara wa masu aikin bautar kasa watau NYSC kudin alawus da ake biya.

Duk wani matashi da ke hidimar kasa a jihar Oyo zai rika karbar N15, 000 a matsayin alawus a kowane wata a maimakon N5, 000 da aka saba biya kafin yanzu.

Gwamna Seyi Makinde ya bada wannan tabbaci ne a ranar Alhamis, 3 ga watan Yuni, 2021, yayin da ziyarci babban sansanin NYSC na jihar Oyo, da ke garin Iseyin.

KU KARANTA: Makinde ya cirewa kowane dalibi 25% na kudin karatu a LAUTECH

Gwamnan ya tabbatar da wannan ziyara da alkawari da ya yi wa masu bautar kasa a shafin Twitter.

“Mun ziyarci sansanin masu hidimar kasa a Iseyin a yamman yau. Na tabbatar wa masu bautar kasa za mu magance matsalolin da shugaban sansanin ya kawo.”

"Na kuma fada masu cewa zan kara alawus dinsu daga N5, 000 zuwa N15, 000.” Inji @Seyimakinde.

Makinde ya ce: “Na kuma ba su labarin yadda na samu aiki a lokacin da nake yi wa kasa hidima a garin Fatakwal, a nan ne kuma na hadu da mata ta, har na aure ta.”

KU KARANTA: Kwamishina ya kira Wike da ‘Dan-daba, Gwamna ya ce masa ‘Barawo’

Ana kiran soke NYSC, Gwamna ya yi alkawarin karawa duk ‘Dan bautar kasar jiharsa alawus
Gwamnan Oyo a sansanin NYSC Hoto: @Seyimakinde
Asali: Twitter

A lokacin da ake kiran a soke NYSC, Mai girma gwamnan ya ce aurensa da Ominini Makinde @iamominini, ya isa misalin yadda tsarin NYSC yake hada-kan jama’a.

Channels TV ta rahoto Makinde yana cewa: “Ni misalin yadda NYSC ke dunkule kasa ne. Ina yi masu fatan alheri.”

A dalilin rashin tsaro, hukumar NYSC ta fara tunanin barin masu yi wa kasa hidima su tsaya su yi aiki a yankunan da suka fito, hakan zai rage cakuduwar da ake samu.

A jiya mun ji cewa tsohon Gwamnan PDP da ya koma APC, Farfesa Ben Ayade, ya yi zaman farko da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa.

Kwanaki da sauya-shekar gwamnan Kuros Ribas, Ben Ayade zuwa APC, Gwamnan ya sa labule da Shugaban kasa. Har yanzu ba a san abin da suka tattauna a kai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng