Gwamnan Borno, Zulum ya gina sababbin gidaje 580 fil, ya rabawa ‘Yan gudun hijira

Gwamnan Borno, Zulum ya gina sababbin gidaje 580 fil, ya rabawa ‘Yan gudun hijira

- Gwamnatin Borno ta rabawa mutane gidajen zama a karamar hukumar Konduga

- Wasu mutanen Auno da suke zama a sansanin gudun hijira sun koma mahaifarsu

- Gwamna Babagana Zulum ya ce ana shaye-shaye da aikin lalata a sansunan IDPs

Mai girma gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da wasu gidaje 580, wadanda nan take a raba wa wadanda suke sansanin gudun hijira.

Jaridar Leadership ta fitar da rahoto cewa wadanda suka amfana da wadannan gidajen, su na rayuwa ne a sansanin gudun hijira na tsawon shekaru.

Farfesa Babagana Umara Zulum ya gina gidajen ne a garin Auno, karamar hukumar Konduga, inda aka yi gajeren biki kafin a rabawa talakawa gidajen.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi gaba da wani 'Dan kasuwa a Kano

Wannan taro da aka shirya a ranar Alhamis, 3 ga watan Yuni, 2021, ya samu halartar jami’an gwamnatin jihar Borno, hakimin Auno da sauran al’umma.

Gwamnatin Babagana Umara Zulum ta raba wa wadannan mutane har su 580 gidajen ne a yunkurin da take yi na ganin mutane sun bar sansanin IDP.

Ma’aikatar da ke da alhakin sake gina gari, samar da matsuguni da habaka jihar Borno ta gina wadannan gidaje da yardar gwamna Babagana Umara Zulum.

Kwamishinan ma’aikatar, Mustapha Gubio da mai ba gwamna shawara wajen taimakawa marasa karfi, Dr. Mairo Mandara ne suka sa ido wajen yin aikin rabon.

KU KARANTA: Mai ba Shugaban kasa shawara ya yi magana a kan ‘United Africa Republic’

Gwamnan Borno, Zulum ya gina sababbin gidaje 580 fil, ya rabawa ‘Yan gudun hijira
Farfesa Babagana U. Zulum Hoto: www.bbc.com/hausa
Asali: UGC

Gwamnan ya gabatar da takardun mallakar gidajen ga wadanda suka dace, kuma ya yi kira ga kwamiti ya yi kokarin ganin ‘yan gudun hijira sun samu matsuguni.

Zulum ya ce ana fama da matsalolin lalata da ‘yan mata, shaye-shaye da cin zarafin jama’a, saboda haka aka rufe sansanin gudun hijira na MOGOLIS da NYSC.

The Nation ta ce mai girma gwamnan Borno, Farfesa Zulum ya bada tabbacin za a dawo karatu a makarantar nan ta Mohammed Goni College of Islamic Legal Studies.

Dazu nan mu ke jin labari cewa miyagun 'yan bindigar da suka sace 'yan makaranta a jihar Neja sun kara kudin fansa daga Naira miliyan 100 zuwa Naira miliyan 200.

Babban malamin makarantar kuma mahaifin wasu yara biyu daga cikin wadanda aka sacen, Abubakar Alhassan, ya bayyana wa manema labarai wannan a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel