Kwankwaso, Tambuwal da ‘Yan siyasan Arewa 6 da za a gwabza da su a zaben 2023

Kwankwaso, Tambuwal da ‘Yan siyasan Arewa 6 da za a gwabza da su a zaben 2023

Tun yanzu manyan ‘yan siyasa da masu fashin baki sun fara lissafi game da babban zaben da za ayi a 2023, idanun mutane da-dama, ya na kan jam’iyyar PDP.

Legit.ng Hausa ta yi nazari wannan karo a kan wadanda ake ganin za su nemi tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamyya ta PDP a zaben 2023.

Mun zakulo jiga-jigan ‘yan siyasan Arewa da ake ganin cewa da za su za a fafata a zabe mai zuwa:

1. Atiku Abubakar

Da alamun cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar zai sake neman takara. Atiku ya na dukiyar da za a bukata domin cin ma wannan buri, baya ga haka, bai da adawa sosai a yankinsa na Arewa maso gabas.

Sai dai Atiku Abubakar ya yi takara sau biyar ba tare da ya kai ga nasara ba, wanda hakan zai iya sa a hana shi tikiti, ganin zai yi wahala ya iya kai labari.

2. Rabiu Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya na cikin ‘yan siyasar da su ka fi kowa farin jini a kasar nan. Amma sai ya yi da gaske zai iya samun kafa da karbuwa cikin manyan jam’iyyar PDP ta yadda zai samu tikiti a zaben 2023.

Ko da cewa darikar siyasar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta Kwankwasiyya ta ratsa jihohin Arewa, ya na da sauran atiki a yankin Kudu.

KU KARANTA: Ana rikici tsakanin Rabiu Musa Kwankwaso da Aminu Tambuwal

3. Aminu Waziri Tambuwal

Ana zargin Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya kwallafa rai sosai a kan kujerar shugaban kasa. Ganin irin namijin kokarin da ya yi wajen neman tikiti a 2019, babu mamaki gwamnan zai jarraba sa’a da kyau a 2023.

Cikin wadannan ‘yan siyasa Tambuwal ne sabon shiga kuma ‘dan autansu, sai dai ana ganin cewa ya na da goyon bayan wasu manyan kasa.

4. Abubakar Bukola Saraki

Bukola Saraki ya na cikin wadanda ake yi wa hangen neman kujerar shugaban kasa a Najeriya. Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya nuna kware wa a siyasa da sanin aiki (kamar Aminu Tambuwal) a lokacin da ya rike majalisar dattawa.

Saraki zai iya fuskantar cikas din da mahaifinsa ya samu, rashin tasirin yankinsa na Arewa maso tsakiya wajen fito da ‘dan takarar shugaban kasa.

5. Attahiru Dalhatu Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ba ya neman kujerar komai a Najeriya sai ta shugaban kasa. Attahiru Dalhatu Bafarawa ya na cikin ‘yan siyasan da su ke da tarin arziki, kuma an dade ana dama wa da shi a siyasar kasa.

Amma watakila tun a gida Bafarawa zai fara gamu wa da cikas daga wajen gwamna mai-ci, Aminu Tambuwal, sannan bai yi wani suna a wajen yankinsa ba.

Kwankwaso, Tambuwal da ‘Yan siyasan Arewa 6 da za a gwabza da su a zaben 2023
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya sallami Ministar kudi inji PDP

6. Sule Lamido

Alhaji Sule Lamido tsohon ‘dan siyasa ne wanda tun zamanin PRP su ka yi fice. Sule Lamido mai shekara 72 ya nuna kwarewarsa a lokacin da ya yi gwamna a jihar Jigawa. Sule ya na cikin masu tsananin kishin jam’iyya, wadanda ba su taba barin PDP ba.

Baya ga shekaru da su ka ja wa Sule Lamido irin Atiku Abubakar, akwai manyan ‘yan siyasan yankinsa da za su iya murkushe shi idan ya yi burin takara.

Kwanaki kun ji cewa tsohon Gwamnan jihar Neja, Dr. Muazu Babangida Aliyu ya bayyana dalilin juyawa Shugaban kasa Goodluck Jonathan baya a zaben 2015.

Dr. Muazu Babangida Aliyu ya bayyana cewa saba wa yarjejeniyar da Jonathan ya yi da Gwamnonin Arewa ya sa su ka hana shi zarcewa a kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel