Ayyi-riri-ri nanaye: Shugaban kasa ya zama Ango a Ingila, ya auri Masoyiyarsa a boye
- Bayan shekaru ana soyayya, Boris Johnson ya auri Carrie Symonds a Landan
- Carrie Symonds ce ta haifawa Firayim Ministan Ingilan yaro a shekarar bara
- Mutane sun sa ran za ayi auren a watan nan, kwatsam sai aka ji har an daura
Firayim Ministan kasar Birtaniya, Boris Johnson ya auri sahibarsa, Carrie Symonds, a wani irin biki da aka gudanar a boye a cocin Westminster a Landan.
Gidan talabijin na CNN ya rahoto cewa an shirya wani karamin biki ne yayin da Boris Johnson ya auri Carrie Symonds ne ba tare da tarin jama’a sun halarta ba.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Symonds mai shekara 33 ta na aiki da wata gidauniya da ake kira Oceana.
KU KARANTA: Buhari ya maidawa Twitter martani a kan goge maganar da ya yi
Mai magana da yawun bakin gidan gwamnatin Birtaniya, ya bayyana cewa ma’auratan za su yi biki domin ‘yanuwa da abokan arziki su taya su murna nan gaba.
Kakakin fadar shugaban kasar ya bayyana wannan aure a matsayin ‘auren sirri’, ya ce abokan kut-da-kut da ‘yanuwan ma’auratan ne kurum suka samu halarta.
Ministar ayyuka da fansho ta kasar Birtaniya, Misis Therese Coffey, ta tabbatar da wannan aure inda aka ji ta fito shafinta na Twitter, ta na taya ango da amaryar murna.
Therese Coffey ta rubuta: “Ina taya ku murnar aurenku @BorisJohnson da @carriesymonds a yau."
KU KARANTA: Babu wata rufa-rufa, matasan mu ne ke kashe jama'a - Gwamna Umahi
Haka zalika Ministar kananan yara ta Ingila, Vicky Ford ta taya Angon da Amaryarsa murna, ta ce annobar COVID-19 ce ta jawo aka rika daga ranar wannan bikin.
An yi wannan aure ne a lokacin da Johnson da Symonds suka tura wa jama’a goron gayyata da nufin cewa za su shiga daga ciki ne a ranar 30 ga watan yulin nan.
A Afrilun 2020 ne Symonds ta haifi ‘dansu na farko wanda aka sa wa suna Wilfred, a watan nan ne kuma idan za a tuna cutar COVID-19 ta kama Firayim Ministan.
Boris Johnson ya yi ta fama da alamomin cutar COVID-19 wadanda su ka hada da zafin jiki. A dalilin haka aka yi maza aka kwantar da shi a wani babban asibiti.
Asali: Legit.ng