An cafke ‘Dan Najeriya ya saci kusan Dala miliyan 1 daga asusun mutane 5,500 a kasar waje

An cafke ‘Dan Najeriya ya saci kusan Dala miliyan 1 daga asusun mutane 5,500 a kasar waje

- FBI ta kama Charles Onus, ta na tuhumarsa da laifin damfarar mutum 5, 500

- Hukumar na zargin Charles Onus ya saci fiye da Naira miliyan 300 a Amurka

- Idan an samu wannan mutumi da laifi a kotu, zai iya shafe shekara 10 a daure

Hukumar FBI mai bincike ta kasar Amurka ta cafke wani ‘dan Najeriya, Charles Onus, bisa zargin damfarar Bayin Allah kudin da sun kai Dala $800, 000.

Premium Times take cewa ana tuhumar wannan mutum, Charles Onus da damfarar mutane, ya rika dauke masu kudi, ya aika zuwa ga katin bankinsa.

Idan aka yi lissafi a yadda ake canjin Dala a yau, kudin da ake zargi Onus ya sata sun haura N320m.

KU KARANTA: FBI ta kama wadanda ake zargi da shirin sace Gwamna

Kamar yadda ma’aikatar shari’a ta kasar Amurka ta wallafa a shafinta na yanar gizo, an kama Onus a garin Francisco tun a ranar 14 ga watan Afilu, 2021.

Mista Onus ya shafe kwanaki 20 ya na tsare, kafin a gurfanar da shi a gaban wani babban kotun tarayya da ke garin Manhattan a ranar Larabar da ta gabata.

Da aka shiga kotu, gwamnatin Amurka ta zargi Onus da laifin kutse cikin akawun din mutane fiye da 5, 500, ta haka ya yi gaba da kudin da ya kusa kai fam $1m.

A jawabin da gwamnatin Amurka ta fitar, ta ce Onus tamkar barawon da ya burma cikin banki ne, sai dai shi ya yi hakan ne ba tare da ya taka kafarsa a ciki ba.

KU KARANTA: Babu abin da ya hada Buhari da neman sake sunan Najeriya - Bashir Ahmaad

An cafke ‘Dan Najeriya ya saci kusan Dala miliyan 1 daga asusun mutane 5,500 a kasar waje
Jami'an FBI Hoto: www.qz.com/africa
Asali: UGC

Ma’aikatar shari’ar ta ce jami’an FBI da IRS-CI ne su ka yi nasarar ram da wannan mutum da yanzu yake kotu, inda ake tuhumarsa da laifi mai girma a doka.

Tsakanin Yulin 2017 zuwa 2018 ake tunanin Onus ya kutsa akawun din wani kamfani, ya canza bayanan bankin ma’aikata, ta yadda ya yi ta gaba da albashinsu.

Idan an samu wanda ake zargi da laifin satar dukiya da yin kutse ta shafin yanar gizo, Nairamtetrics ta ce zai iya yin zaman gidan yari na shekaru goma.

Labarin Charles Onus ya na zuwa ne bayan an damke wani hadimin gwamnan jihar Ogun, Abidemi Rufai, da laifin makamancin irin wannan laifi a Amurka.

Idan za ku tuna, Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya dakatar da Abidemi Rufai daga aiki bayan ya ji labarin cewa an cafke mai ba shi shawarar a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel