FBI ta kama wadanda ake zargi da shirin sace Gwamnar Michigan, Whitmer

FBI ta kama wadanda ake zargi da shirin sace Gwamnar Michigan, Whitmer

- Dakarun FBI sun ce akwai masu kutun-kutun din tumbuke Gwamnonin Amurka

- Wadannan Miyagun su na zargin wasu Gwamnoni ba su bin kundin tsarin mulki

- Gwamnar Michigan, Gretchen Whitmer ta na cikin wadanda ake nufin kai wa hari

Hukumar bincike ta FBI ta kasar Amurka, ta ce ta gano wani mugun shiri da aka kitsa na yin awon-gaba da gwamnar jihar Michigan, Gretchen Whitmer.

Gidan talabijin na CNN ta fitar rahoton cewa FBI ta ce akwai wasu miyagun da aka samu su na shirin kifar da Gwamnonin jihohi a kasar Amurka.

Daga cikin wadanda ake shirin hambararwa, har da mai girma gwamna Gretchen Whitmer.

KU KARANTA: Trump ba Kirista ba ne - Fafaroma

FBI ta ce wasu mutane shida aka kama da ake zargi da wannan laifi. Masu shirin su na zargin gwamnonin da sabawa kundin tsarin mulkin Amurka.

Jami’an FBI sun bayyana sunayen wadanda ake zargin da; Adam Fox, Ty Garbin, Kaleb Franks, Daniel Harris, Brandon Caserta da kuma Barry Croft.

Tun farkon shekarar nan aka fara samun kishin-kishin na wannan mugun labari a kafafen sadarwa na zamani, daga nan FBI ta fara binciken lamarin.

Dakarun FBI sun riga shiga a boye domin gano asirin masu wannan shiri. A haka ne har su ka halarci wani taro da aka shirya da wannan nufi a Ohio.

KU KARANTA: Abin da Trump ya tambayi Likitoci bayan ya kamu da COVID-19

FBI ta kama wadanda ake zargi da shirin sace Gwamnar Michigan, Whitmer
Gwamnar Michigan, Whitmer Hoto: Getty Images
Asali: UGC

A watan Yunin da ya gabata ne wadannan miyagu su ka zauna domin tsara yadda za su kifar da gwamnatocin jihohi da su ke zargin su na sabawa dokar kasa.

Ana zargin gwamnar Michigan da daukar matakai masu tsauri wajen yaki da COVID-19. Gwamnar mai shekara 49 ta na cikin ‘yan adawar Donald Trump.

A ranar Alhamis kun ji cewa wani Alkalin Kotu a kasar Yemen ya yankewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump da Sarakunan Saudi hukuncin kisa.

An yanke hukuncin ne a dalilin harin saman da aka kai a garin Majz wanda ya kashe yara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel