IPOB sun jawo ‘Yan kasuwan Kano sun yi asarar dukiyar kusan Naira Miliyan 100 a kiftawar ido

IPOB sun jawo ‘Yan kasuwan Kano sun yi asarar dukiyar kusan Naira Miliyan 100 a kiftawar ido

- Ana zargin ‘Yan kungiyar IPOB da tare motocin manjan ‘Yan kasuwan Kano

- Direbobin sun tsere, sannan an kona duk wata dukiya da motocin suka dauko

- Shugaban ‘yan kasuwan Galadima Road Traders ya ce an dade ana irin haka

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Galadima Road Traders na jihar Kano, Mustapha Shu’aibu Sulaiman, ya bayyana irin asarar da suka gamu da ita.

Mustapha Shu’aibu Sulaiman ya yi magana da Daily Trust, inda ya shaida cewa wasu da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne sun yi sanadiyyar rasa dukiyoyinsu.

Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman ya ce dakarun IPOB ake zargin sun kai wa motocinsu da suka dauko manja daga kudu maso gabas zuwa garin Kano hari.

KU KARANTA: Matasan Ibo ke kai hare-hare a Kudu - Gwamna Umahi

“An kai wa wasu manyan motoci biyu makil da suka dauko manja na mutanen kungiyarmu hari a garin Nsukka, jihar Enugu.” Inji Mustapha Shu’aibu Sulaiman.

Shu’aibu Sulaiman ya ce motocin suna kan hanyarsu ne na zuwa Kano daga kasar Ibo a ranar Lahadi. Ba wannan ne karon farko da irin hakan ya faru ba.

A cewar shugaban ‘yan kasuwar, motocin biyu suna dauke da jarkoki 2544 na manja, daya ya dauko jarkoki 1056, sai kuma dayan yana dauke da jarkoki 1488.

“Da aka tare wadannan motoci, sai direbobinmu suka tserewa ransu, suka shige cikin jeji. A haka ne ‘yan kungiyar na IPOB suka sa wuta, suka kona motocin.”

KU KARANTA: 'Yan ta'addan IPOB sun kashe Hausawa a jihar Imo

IPOB sun jawo ‘Yan kasuwan Kano sun yi asarar dukiyar kusan Naira Miliyan 100 a kiftawar ido
Shugaban ‘Yan kasuwa, Galadima Road Traders, Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Da aka tambayi wannan ‘dan kasuwa game da darajar dukiyar da su ka rasa a harin, sai ya ce: “Darajar duka kayan da motocin ya haura Naira miliyan 80.”

Sulaiman ya ce: “Kayan na ‘yan kungiyarmu ne, su kusan 50 wanda mafi yawansu kananan ‘yan kasuwa ne, wasu daga cikinsu suna da jarkoki 20 ne ko 50 kurum.”

All Africa ta ce abin ya kai wasu cikin wadannan ‘yan kasuwa da sun rasa duk abin da suka mallaka a harin sun fara tunanin maida martani, aka shawo kansu.

A wajen sauraron yi wa tsarin mulki kwaskwarima, wani ya bada shawarar a canza sunan Najeriya zuwa United African Republic ko United Alkebulan Republic.

Mabiya Twitter sun yi kaca-kaca da yunkurin maida sunan kasar nan United African Republic a shafukansu, suka ce sauyin suna ba shi ne abin da zai gyara Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel