Siyasa: Gwamna Wike da tsohon Kwamishinansa sun barke da cacar-baki a gaban kowa
- John Bazia ya caccaki Nyesom Wike da suka hadu a wani shirin gidan talabijin
- Tsohon Kwamishinan yace Gwamnan ya na abubuwa ne kamar wani ‘Dan-daba
- Gwamnan Ribas ya yi raddi, yace Bazia ya taba satar goron da ya ke Kwamishina
Mai girma Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da tsohon kwamishinansa, John Bazia, sun buge da cacar baki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, 2021.
Punch ta ce gwamna Nyesom Wike da John Bazia sun gwabza ne a lokacin da suka bayyana a gaban shirin Politics Today a gidan talabijin na Channels.
Kamar yadda muka samu labari, Bazia ya yi magana a game da sauya-shekar da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP su ke yi, suna koma wa APC a jihar Ribas.
KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta na shirin rasa Gwamnan na 3 zuwa APC a shekara 2
“Duk wadanda suke tare da gwamna Wike, in fada maku sun san halin da suke ciki. Amma kuna ganinsu a talabijin, kuna ganin abubuwan da yake yi a kasa.”
“Wani lokacin sai ka rika tunani wannan mutum ne mai ilmi daya waye; abubuwan da yake yi, ya na nuna kamar ya manta yana rike da mukami.” Inji Bazia.
Vanguard ta ce Bazia bai tsaya a nan ba, ya ce gwamnan ya na yin al’amura kamar wani ‘dan daba. Da jin wannan sai ‘dan jarida ya taka wa 'dan siyasar burki.
Seun Okinbaloye ya bukaci gwamnan ya maida martani, a fusace, sai ya ce: “Ka na nan zaune kana cewa in maida martani ga mutumin da na ba Kwamishina.”
KU KARANTA: Twitter: Don mene za a goge bayanina, a bar na Nnamdi Kanu - Buhari
“’Dan-daba ya nada ka Kwamishina, ba ka san ‘dan-daba ba ne, sai bayan tsige ka. Ka na ta aiki da ‘yan daba, sai da ka ga cewa ba za a dawo da kai a 2019 ba.”
“Dubi irin mutanen da ka ke cewa in maidawa martani. Mutumin da ya sace goron Sarakuna, kuma har yau bai kalubalanci wannan zargi a kotu ba.” Inji Wike.
Bazia ya ce ba za a kamanta gwamna mai-ci, Wike, da tsohon Gwamna Rotimi Amaechi ba..
Bayan zaben 2019 ne John Bazia ya rasa mukaminsa a gwamnatin Ribas, daga nan ya fice daga jam’iyyar PDP mai mulki, Wike ya ce Bazia ya nemi a dawo da shi.
John Bazia ya rike kwamsihinan harkokin kananan hukumomi da masarautu a gwamnatin Nyesom Wike. Daga baya ya zama babban 'dan adawan gwamnan.
Asali: Legit.ng