Ministan Najeriya ya maidawa Twitter martani bayan sun goge maganar Shugaba Buhari

Ministan Najeriya ya maidawa Twitter martani bayan sun goge maganar Shugaba Buhari

- Gwamnatin Tarayya ta soki matakin Twitter na soke maganar Shugaban Najeriya

- Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya zargi kamfanin da nuna son kai

- Lai Mohammed ya ce a baya Twitter ta bar Nnamdi Kanu ya na tunzura al’umma

Gwamnatin tarayya ta ce tana zargin Twitter bayan kamfanin sadarwar zamanin ya goge wani bayani da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi.

A wasu sakonni da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika a dandalin Twitter, ya ja-kunnen ‘yan bana-kwai da suke kokarin jawo sabon yakin basasa.

Bayan an kai wa kamfanin Twitter kuka, sun goge maganar da shugaban kasar ya yi a ranar Talata.

KU KARANTA: Shugaban Majalisar Kano ya shigo Najeriya da takardun COVID-19 na bogi

Jaridar Daily Trust ta rahoto Ministan yada labarai na kasa, Alhaji Lai Mohammed, ya na maida wa Twitter martani, yana zargin kamfanin da rashin adalci.

Alhaji Lai Mohammed yake cewa Twitter sun yi mursisi a lokacin da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu yake aika sakonnin da suke tunzura al’umma.

A cewar Ministan, Twitter ba ta ga dalilin goge sakonnin Nnamdi Kanu da suka yi sanadiyyar kashe ‘yan sanda da aka rika yi a yankin Kudancin Najeriya ba.

Haka zalika, Lai Mohammed ya zargi Twitter da nuna irin wannan son-kan a lokacin da aka yi zanga-zangar EndSARS wanda a karshe lamarin ya zama ta’asa.

KU KARANTA: Twitter ya goge maganar da Buhari ya yi

Ministan Najeriya ya maidawa Twitter martani bayan sun goge maganar Shugaba Buhari
Lai Mohammed Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

The Guardian ta ce Ministan yayi mamakin yadda kamfanin ke ganin akwai matsala a bayanin da shugaban kasar ya yi, ya ce gwamnati ba za ta zama sakarya ba.

Ministan yake cewa: “Wata kungiya ta na bada umarni ga ‘ya ‘yanta su kai hari a ofishin ‘yan sanda, su kashe jami’an tsaro, su kai farmaki a gidajen yari, a kashe gandurobobi, amma kuna cewa shugaban kasa ba zai iya magana domin ya nuna fushinsa ba?"

“Babu wani wuri a Duniya inda wani mutum zai fada wa yaransa su kai wa hukuma hari, babu dalilin da za a bada umarni a kashe ‘yan sanda ko wani.” Inji sa.

A yau ne muke samun labari cewa wasu ‘Yan taware sun bayyana daga cikin Jam’iyyar APC a Jihar Kano, sun fara shiryawa yadda za su yaki Abdullahi Ganduje.

Tsohon 'dan a-mutun Buhari, Alhaji Abdulmajid ‘Dan Bilki Kwamanda ne ya kafa kungiyar da ake kira da APC Akida a cikin tafiyar jam’iyyar APC na reshen jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel