Annobar COVID-19: Boris Johnson ya fara jinya a asibiti – Gwamnatin Ingila
Kwanakin baya kun ji labari an gano Firayim Ministan Birtaniya, Boris Johnson ya na dauke da kwayar cutar COVID-19. A wancan lokaci alamomin cutar ba su bayyana ba tukuna.
Yanzu mun samu labari daga BBC cewa an kwantar da Firayim Ministan na Ingila a asibiti. Rahotonni sun ce an kai shugaban wani asibiti ne a Landan a karshen makon da ya wuce.
Boris Johnson ya na ta fama da alamomin wannan cuta ta COVID-19 wanda su ka hada da zafin jiki. A dalilin haka ne aka yi maza aka dauki matakin yakar wannan cutar hana numfashi.
Gwamnatin Ingila ta bayyana cewa rigakafi aka yi domin hana cutar tasiri a jikin Firayim Ministan. Duk da cewa ya na kwance a asibiti, Johnson ne ya ke jan ragamar gwamnati.
Ana sa ran cewa Ministan harkokin kasar waje ne zai jagoranci wani taro da za a yi a Ingila a kan annobar COVID-19. Kawo yanzu dai babu mamaki an yi wannan taro dazu a birnin Landan.
KU KARANTA: COVID-19: An yi makokin mutuwar mutane 1300 a sa’a 48 a Ingila
Misis Laura Kuenssberg da ke aiki a BBC ta bayyana cewa akwai yiwuwar Boris Johnson ya kwana a asibiti. Laura Kuenssberg ta ce Likitoci za su yi wa shugaban wasu gwaje-gwaje.
Wannan ya zo daidai da jawabin da ya fito daga bakin Mai magana da yawun Firayim Ministan a Landan. Jawabin ya nuna cewa Likitoci ne su ka bada shawarar a kwantar da Johnson.
“Wannan matakin rigakafi ne ganin Firayim Ministan ya cigaba da nuna alamun cutar Coronavirus, kwanaki goma bayan an yi masa gwaji kuma an gano ya kuma da cutar.”
“Firayim Ministan ya godewa Ma’aikatan lafiya da irin namijin kokari da jajircewarsu, sannan kuma ya yi kira ga Jama’a su bi shawarar da gwamnati ta bada na zama a cikin gida.”
Tun daga lokacin da wannan cuta ta kama Boris Johnson, ya na aiki ne daga gida. A Ranar 27 ga Watan Maris ne sakamakon gwajin da aka yi ya nuna Johnson ya kamu da cutar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng