Yaki da rashin gaskiya da Gwamnatin Buhari ta ke yi, ya shiga Kwastam, za a rika binciken kowa
- Jami’an kwastam za su rika bayyana kadarorin da suka mallaka a Najeriya
- Gwamnati za ta rika bibiyar dukiyar kowane ma’aikacin hukumar kwastam
- Ma’aikacin da ya yi karya ko ya wawuri kudi zai gamu da dauri a kurkuku
Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa shugaban hukumar kwastam na kasa da ma’aikatansa za su rika bayyana duk wasu kadarori da suka mallaka.
An dauki wannan mataki ne yayin da gwamnatin tarayya ta fadada yaki da rashin gaskiya da ta ke yi.
Ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ke da nauyin wannan aiki za a daura wa dawainiya da alhakin bibiyar dukiyar da jami’an kwastam suka tara.
KU KARANTA: Shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali ya yi aure
Kamar yadda rahoton da aka fitar a ranar Laraba ya bayyana, wannan bincike da aka kawo ya shafi daukacin ma’aikatan hukumar mai yaki da fasa-kwauri.
Har yanzu ba a sa ranar da za a soma wannan aiki ba, amma duk wani ma’aikacin kwastam zai bayyana kadarar da dukiyar da yake da ita yadda doka ta ce.
Jami’an gwamnatin zasu bayyana kadarorin da suka mallaka a takardar da aka tanada domin wannan, kamar dai yadda aka bukaci ma’aikatan banki su rika yi.
Idan aka samu jami’i ya yi karya a fam din da ya cika, ko ya yi karya game da harkar fita ko shigo da wasu kaya, zai iya shafe shekaru 10 yana daure a kurkuku.
KU KARANTA: Hameed Ali ya nada sababbin DCGs 2, ACGs 5 a Kwastam
Haka duk wani ma’aikacin hukumar kwastam da aka samu ya na rayuwar da ta fi karfin abin da yake samu a wajen aiki, zai fuskanci daurin har na shekaru 10.
Ana jiran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan yadda wannan doka za ta rika aiki a gidan kwastam irin yadda aka shiga da ita bankuna.
Shugaban kasa ya na da ikon kawo dokar da za ta tursasa wa kowane irin ma’aikacin gwamnatin tarayya ko kamfani mai zaman kansa ya bayyana dukiyarsa.
A jiya aka ji Gwamna Seyi Makinde ya rage kudin karatu a LAUTECH, bayan rage kudin, Gwamnan ya dawo da wasu Ma’aikata 170 da aka sallama a aiki.
Amma a jihar Kaduna, Gwamnatin Nasir El-Rufai ta yi sama da kudin karatun jami’a da kusan 400%, hakan ya sa wasu dalibai su ka fita suna yin zanga-zanga.
Asali: Legit.ng