Hotuna: Shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali ya angwance
- Shugaban hukumar kwastam na kasa, Hameed Ali ya angwance a ranar Asabar, 30 ga watan Mayu
- Shagalin bikin shugaban hukumar kwastam din an yi shi ne a Kano amma babu wata gayya da aka tara
- Ya kara auren ne bayan shekaru biyu da mutuwar uwargidansa, Hajiya Hadiza Jummai a garin Abuja
Hameed Ali, shugaban hukumar kwastam ta kasa, ya angwance da sabuwar matarsa a jihar Kano.
Bikin wanda aka yi shagalinsa a ranar Asabar, an yi shi ne bayan kusan shekaru biyu da rasuwar uwargidansa Hajiya Hadiza Jummai.
Hajiya Jummai ta rasu yayin da take da shekaru 53 a garin Abuja. Ta rasu a ranar 29 ga watan Oktoban 2018.
Allah ya albarkaci aurensa da 'ya'ya hudu.
An nada Ali matsayin shugaban hukumar kwastam na kasa a ranar 27 ga watan Augustan 2015, bayan hawan shugaban kasa Muhammadu Buhari mulkin Najeriya.
Har a halin yanzu shine shugaban hukumar kwastam na kasa.
A shekarar 2017, Ali mai shekaru 65 din ya hau kanun labarai bayan da ya ki bayyana gaban majalisar dattijan kasar nan da khaki kamar yadda aka bukata.
KU KARANTA: Gwamna Bauchi ya bayyana wani babban al'amari da ke faruwa da shi
A wani labari na daban, Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi, ya ce yana fama da mummunan kalubale da adawa tun bayan da ya hau kujerar shugabancin jihar.
A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Asabar bayan cikarsa shekara daya a kan karagar mulkin jihar, Mohammed ya ce yana fama da wasu mutane da suka hade masa kai duk da ya taba aiki tare da su kafin ya zama gwamna.
"Muna iyakar kokarinmu wajen aiki ba don a jinjina mana ba, muna yi ne don sauke nauyin da ke kanmu," Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito.
"Kwamishinoni na na korafi amma dole ne mu sadaukar da wasu abubuwan don nuna godiya ga Allah da kuma jama'ar jihar Bauchi da suka zabe mu.
"Ina fama da kalubale amma kuma jama'ar sun yarda dani. Ina fama da adawa don ko a yanzu akwai wadanda suka hade min kai," yace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng