Yayin da El-Rufai ya yi karin 350% a kudin Jami’a, wani Gwamna ya yi wa kowani Dalibi ragi

Yayin da El-Rufai ya yi karin 350% a kudin Jami’a, wani Gwamna ya yi wa kowani Dalibi ragi

- Seyi Makinde ya ce an cirewa kowane dalibai 25% na kudin karatu a LAUTECH

- Gwamnan ya ce jihar Oyo ta karbe duk mallakar jami’ar daga hannun jihar Osun

- Bayan haka, Gwamnatin Makinde ta dawo da wasu Ma’aikata da aka kora a aiki

A ranar Talatar nan ne muka ji cewa Mai girma gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya ziyarci jami’ar fasaha ta Ladoke Akintola da ke Ogbomoso.

Channels TV ta ce Gwamnan ya bada sanarwar rage kudin makarantar ne a lokacin da ya ke zanta wa da wasu daga cikin daliban makaranta a garin Ogbomoso.

Seyi Makinde ya ce wannan ragin kudin karatu da aka yi zai shafi kowane dalibi da ke karatu a LAUTECH, ba tare da la’akari da inda ya fito ko matsayinsa ba.

Babban sakataren yada labarai na gwamnan Oyo, Mista Taiwo Adisa, ya fitar da wannan jawabi a jiya.

KU KARANTA: Kudin makaranta: Malamai ba su goyon bayan Gwamna El-Rufai

Makinde ya ce:

“Na ji dadin dawo wa cikinku, bayan zaben shekarar 2019, ya kamata in zo in yi maku godiya, amma ban so in zo ba tare da na cika alkawarin da na yi ba."

Alkawarin da ‘dan takarar gwamnan a wancan lokaci ya yi shi ne gwamnatinsa za ta karbe mallakar jami’ar daga yarjejeniyar da aka shiga da jihar Osun.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana da kansa a shafin Twitter (@SeyiMakinde), ya ce ya rage 25% daga cikin abin da ‘daliban jami’ar suka saba biya a duk shekara.

“Bari in fada maku, kudin karatun LAUTECH shi ne mafi araha a daukacin Kudu maso yamma duk da haka. Bayan haka, zan rage kudin makaranta ga kowa, ‘yan jiha da baki, har da sababbin dalibai, za a yi ragin 25% a kan kowane dalibi.” Inji gwamnan.

Yayin da El-Rufai ya yi karin 350% a kudin Jami’a, wani Gwamna ya yi wa kowane Dalibai ragi
Gwamna Seyi Makinde a LAUTECH Hoto: @Seyimakinde
Asali: Twitter

KU KARANTA: Daga N26, 000, Wasu daliban KASU za su koma biyan N500, 000

Har ila yau, gwamnatin Seyi Makinde ta sa danban gina wani sashe a asibitin koyar da aikin likita na jami’ar, sannan ya dawo da ma’aikata 170 da aka kora a aiki.

Gwamnan ya ce za a biya ma’aikatan da aka dawo da su albashin watanni biyar da suka wuce. A karshe ya ce zai gina gadar sama saboda rage cinkoso a Ogbomosho.

A jihar Kaduna kuwa, gwamnatin Nasir El-Rufai ta kara kudin karatu a jami’ar jiha ta KASU, wanda hakan ya sa ‘dalibai da sauran jama’a suke ta yin zanga-zanga.

A ranar Talatar nan ‘daliban jami'ar jihar Kaduna, KASU, su ka gudanar da zanga-zanga, inda suka tare manyan titunan da ke jihar, suka je har gaban gidan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel