2023: APC ta bangare a Kano, ‘Dan-a-mutun Buhari ya kafa APC-Akida, za su yaki Ganduje
- Abdulmajid ‘Dan Bilki Kwamanda ya kafa tafiyar APC Akida a Jihar Kano
- ‘Dan Bilki Kwamanda ya ce ba za su yarda da kakaba ‘Yan takara a 2023 ba
- ‘Dan siyasar ya nuna cewa Barau Jibrin suke goyon baya ya zama Gwamna
Jaridar The Cable ta samu rahoto cewa Alhaji Abdulmajid ‘Dan Bilki Kwamanda, ya kafa kungiya a cikin tafiyar jam’iyyar APC na reshen jihar Kano.
Abdulmajid ‘Dan Bilki Kwamanda wanda fitaccen ‘dan gani-kashe nin shugaba Muhammadu Buhari ba ne, shi ne ya ke jagorantar ‘Yan APC Akida.
Tun a 2002, Abdulmajid ‘Dan Bilki Kwamanda yake tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wancan lokaci ya na ‘dan jam’iyyar hamayya ta APP.
KU KARANTA: Dan Bilki Kwamnada ya ce Buhari ya rasa farin jini a Najeriya
Da yake magana da ‘yan jarida a ranar Talata, 1 ga watan Yuni, 2021, ‘Dan Bilki Kwamanda ya ce sun yanke shawarar kirkiro tafiyar APC Akida a Kano.
‘Dan siyasar ya ce sun kafa wannan bangare na taware ne a ranar Litinin, 31 ga watan Mayu, 2021.
Manufar kafa wannan taware a APC shi ne hana gwamna Abdullahi Umar Ganduje kakaba wa mutanen jihar Kano ‘yan takara a jam’iyyar APC a 2023.
“Kokarin da gwamnan, da shugaban rikon-kwarya suke yi na hana wasu ‘yan a-mutun jam’iyya shiga takarar gwamna ya saba wa tsarin siyasa.” Inji shi.
KU KARANTA: 'Dan Bilki ya soki zabin Ministan da Buhari ya yi a Kano

Asali: UGC
“Mun riga mun tsara tafiyarmu, da yadda za mu tabbatar cewa ‘dan APC Akida ya shiga gidan gwamnati a zaben 2023.” Inji Alhaji ‘Dan Bilki Kwamanda
“Mun kafa APC Akida, kuma kashi 100% na mutanen Kano suna tare da mu, ko shugaba Muhammadu Buhari ba zai hana mu bangarewa ba a yanzu."
Kwamanda ya ce ‘Yan APC Akida ba su yarda da kama-karyar gwamna da Abdullahi Abbas ba, sannan ya ce ‘dan takarar gwamnansu shi ne Barau Jibril.
A makon nan kun ji cewa wasu shugabannin APC a Kazaure sun dawo da Hon. Gudaje Kazaure cikin jam’iyya, sun soki wadanda da suka dakatar da shi.
Wadannan shugabanni na APC sun ba ‘Dan Majalisar tarayyar hakuri, su ka ce har gobe ya na nan a matsayinsa na 'dan jam'iyyar mai mulki a jihar Jigawa.
Asali: Legit.ng