Tirkashi: Ko masinja bai kamata shugaba Buhari ya bawa Nanono ba, balle minista - Dan Bilki Kwamanda

Tirkashi: Ko masinja bai kamata shugaba Buhari ya bawa Nanono ba, balle minista - Dan Bilki Kwamanda

- Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda wanda yake dan a mutun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne, ya ragargaji Sabo Nanono

- A cewar Kwamanda Sabo Nanono mutum ne da bai cancanci a ba shi amana ba

- Kwamanda ya jaddada cewa zai je Abuja domin ganawa da shugaba Buhari don ba shi shawarar janye wannan kudiri

A wata hira da yayi a wani shirin siyasa na gidan rediyon Rahma dake jihar Kano, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda wanda yake dan a mutun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne, ya ragargaji Sabo Nanono wanda shugaba Buhari ya aika da sunansa ga majalisar tarayya domin ta tantanceshi a cikin jerin sabbin Ministoci.

A cewar Kwamanda Sabo Nanono mutum ne da bai cancanci a ba shi amana ba, saboda kasancewar an san halinsa tun daga kan tsohon Bankin Arewa wato (Bank Of The North) kana kuma wanda suka ci moriyar farin jinin Buhari don biyan bukatun kansu.

Kwamanda ya jaddada cewa zai je Abuja domin ganawa da shugaba Buhari don ba shi shawarar janye wannan kudiri na ba Nanono Minista.

KU KARANTA: Yadda aka kusa yi min auren dole, lokacin ina 'yar shekara 13 - Jaruma Rahama Sadau

"Na fada na kuma fada bai dace da wannan mukami ba". Dan Bilki ya jaddada maganarsa.

A wannan makon ne dai shugaban kasar ya fitar da kimanin sunayen mutum hamsin, inda ya mikawa majalisar dattawa akan ta tantance su a matsayin mutanen da ya zaba su zama ministocinsa.

Wadannan sunaye da shugaban kasar ya fitar sun jawo kace nace a shafukan sada zumunta, inda mutane da yawa da jam'iyyun adawa suka yo caa akan shugaban kasar akan wadannan mutane da ya fitar basu cancanci a basu kujerun minista ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel