Da Buhari zai sake tsayawa takara babu mai zabensa - Jigo a APC, Dan Bilki Kwamnada

Da Buhari zai sake tsayawa takara babu mai zabensa - Jigo a APC, Dan Bilki Kwamnada

- Jigo a APC, Abdulmajid DanBilki Kwamanda ya ce shugaba Buhari ya rasa fiye da kaso hamsin na farin jininsa a wurin talaka

- Ya ce babu shakka Buhari zai fadi zabe da a ce yana da damar kara tsayawa takarar shugaban kasa

- Kwamanda ya yi kaurin suna wajen kare shugaba Buhari tare da tallata manufofinsa, musamman a Kano

Abdulmajid Danbilki Kwamanda, jigo a jam'iyyar APC sannan fitacce wajen goyon baya da tallata manufofin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi magana a kan salon mulkin gwaninsa a halin yanzu.

A wata hira da aka yi da shi a gidan radiyon 'Vision FM' da ke birnin Kano, Kwamanda ya ce babu shakka shugaba Buhari ba zai sake cin zaben shugaban kasa ba da a ce yana da damar sake tsayawa takara nan gaba.

Ya bayyana hakan ne ranar Asabar, kamar yadda jaridar yanar gizo da ke Kano, labarai24, ta wallafa ranar Lahadi.

Kwamanda ya kara da cewa shugaba Buhari ya rasa fiye da kaso hamsin na farin jinin da ya ke da shi a wurin talaka.

Da Buhari zai sake tsayawa takara babu mai zabensa - Jigo a APC, Dan Bilki Kwamnada
Buhari da Dan Bilki Kwamnada Hoto: Labarai24
Asali: UGC

Kalaman na Kwamanda na zuwa a daidai lokacin da jama'a, musamman a arewacin Najeriya, ke korafi a kan shirun da shugaba Buhari ya yi a kan ta'adin da 'yan bindiga ke tafkawa a jiharsa ta Katsina.

DUBA WANNAN: An raunata mutane 8 yayin rikici tsakanin 'yan Izala da Tijjaniyya a kan limancin Masallacin Juma'a

Jama'a da dama sun yi mamakin jin Kwamanda ya na furta irin wadannan kalamai da bakinsa, musamman saboda sanin da aka yi ma sa wajen goyon bayan Buhari.

Da yawa na ganin cewa hakan wata alama ce da ke nuna cewa Kwamanda ya fara karaya da al'amuran gwaninsa da ya tallatawa jama'a a dukkan lokuta baya da ya yi takarar shugaban kasa a jam'iyyu daban - daban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel