Rikita-rikita: Wasu Shugabannin APC sun kashe dakatarwar da aka yi wa Gudaji Kazaure

Rikita-rikita: Wasu Shugabannin APC sun kashe dakatarwar da aka yi wa Gudaji Kazaure

- An samu Shugabannin APC da suka soki dakatarwar da aka yi wa Gudaji Kazaure

- Mataimakin Shugaban jam’iyya na Kazaure, Bello Sanda, ba su goyon bayan hakan

- Bangaren Sanda sun ce za su binciki wadanda suka zartar da wannan danyen aiki

Jam’iyyar APC ta reshen jihar Jigawa ta janye dakatarwar da aka yi wa ‘dan majalisa mai wakiltar yankin mazabun Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi.

A yau ne Jaridar Punch ta rahoto cewa jam’iyyar ta APC mai mulki ta soke matakin da aka dauka a baya na hukunta Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure.

Mataimakin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC a mazabar ‘dan majalisar tarayyar, Bello Sanda, ya aikawa kwamitin jam’iyya na Mai Bala Buni takarda.

KU KARANTA: Jam'iyar APC ta dakatar da Kazaure saboda ya soki Gwamnati

Premium Times ta ce kashi biyu cikin uku na shugabannin mazabu da na kananan hukumomin da ‘dan majalisar yake wakilta sun yi tir da wannan dakatarwa.

A wannan wasika, Bello Sanda ya ce akasarin shugabannin jam’iyya da ke karamar hukumar Kazaure da shugabannin mazabu 21 daga cikin 27 suna tare da su.

Sanda ya yi wa wannan takarda da ya aika wa uwar jam’iyya take da: ‘Forwarding the Resolution by the Two-Third Majority of the APC Kazaure Local Government Area Party Executives, six out of eleven wards’

“Muna sukar dakatarwar da aka yi wa ‘dan majalisarmu kuma jagoranmu da muke girmamawa, Honarabul Mohammed Gudaji Kazaure.” Inji 'yan bangaren Sanda.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya jefar da wasu tulin kudirorin Sanatoci

Rikita-rikita: Wasu Shugabannin APC sun kashe dakatarwar da aka yi wa Gudaji Kazaure
Gudaji Kazaure ya soki Gwamna Muhammad Badaru Hoto: guardian.ng
Asali: Depositphotos

A cewar wannan bangare, dakatar da Hon. Mohammed Gudaji Kazaure daga jam’iyyar da ake yunkurin yi, ya saba wa doka, kuma ba a bi tsarin mulkin APC ba.

Shugaban jam’iyya, mai bada shawara a kan shari’a da wasu mutum biyu suka dauki wannan mataki, Sanda ya ce an ci albasa da bakunan sauran shugabannin.

A karshe, takardar ta ce: “Mun yi da-na-sanin faruwar wannan abin kunya, amma jam’iyya za ta binciki shugaban APC da sauran jami’ai ukun ba tare da bata lokaci ba.”

A baya kun ji cewa kungiyar SMBLF ta yi taro, inda ta yanke shawara lokaci ya yi da Mutumin Kudu zai zama Shugaban Najeriya bayan wa'adin gwamnati mai-ci.

Kungiyar ta manyan ‘Yan Kudu da Arewa tana so a kawo sabon tsarin mulki, sannan ta bukaci gwamnatin Muhammadu Buhari ta haramta kiwon dabbobi a fili.

Asali: Legit.ng

Online view pixel