An Bayyana Ranar Da Gwamnan Zamfara Matawalle Zai Koma Jam'iyyar APC

An Bayyana Ranar Da Gwamnan Zamfara Matawalle Zai Koma Jam'iyyar APC

- Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle na shirin komawa jam'iyyar All Progressives Congress APC

- Wata majiya kusa da gwamnan ta ce a ranar 12 ga watan Yuni ne gwamnan zai koma APC

- Majiyar ta ce sauke kwamishinoni da sauran masu mukaman siyasa da gwamnan ya yi na cikin shirin sauya shekara

Saukar da kwamishinoni da sauran masu rike da mukaman siyasa da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya yi a ranar Talata na daga cikin shirye-shiryen sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), wata majiya kusa da gwamnan ta fada wa Premium Times.

A cewar majiyar, wacce ta nemi a sakaya sunanta saboda ba a bada izinin magana kan batun ba, Mr Matawalle zai sanar da komawarsa jam'iyyar APC a hukumance a ranar 12 ga watan Yuni, yayin bikin ranar Demokradiyya.

Gwamnan Zamfara Matawalle Zai Koma APC a ranar 'June 12', Majiyoyi
Gwamnan Zamfara Matawalle Zai Koma APC a ranar 'June 12', Majiyoyi. Hoto: @thecableng
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Za a Fara Bawa Malaman Makarantun Allo Shaidar Karatu Ta ‘NCE’ a Kaduna

Majiyar ta ce gwamnan ya sauke kwamishinoninsa da sauran masu mukaman siyasa ne domin mataimakinsa, Mahdi Aliyu, na jan kafa kan batun komawa APC tare da shi.

An dade ana ta jita-jitar cewa gwamnan na son barin jam'iyyar PDP ya koma APC duk da cewa wasu shugabannin APC a jihar ba su son ya dawo jam'iyyar.

A ranar Talata, ya sauke sakataren gwamnatinsa, SSG, Bala Bello da kwamishinoni 23, shugaban ma'aikatan fadarsa, Bala Mande da mataimakin shugaban ma'aikatan fadarsa, Bashir Maru.

Biyo bayan hakan, majiyoyi da suka yi magana da Premium Times sun ce gwamnan zai fice daga PDP a ranar 12 ga watan Yuni.

KU KARANTA: An Haramta Shan Taba Sigari a Bainar Jama'a a Jihar Kano

Matawalle na son ya koma APC kafin a yi babban taron jam'iyyar a watan Yuni. Domin samun hallartar taron, akwai bukatar ya yi rajista a jam'iyyar da ake yi a halin yanzu.

An sanar Matawalle a matsayin gwamna ne a ranar 24 ga watan Mayun 2019, bayan kotun koli ta soke dukkan yan takarar APC saboda rashin yin zaben cikin gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164