Da duminsa: Gagarumar Gobara ta lashe fitaccen katafaren otal a Ikeja, Legas

Da duminsa: Gagarumar Gobara ta lashe fitaccen katafaren otal a Ikeja, Legas

A ranar Litinin da yammaci ne gagarumar gobara ta tashi a otal din Mokland dake lamba 3/9 titin Olakoleosho dake Ikeja a jihar Legas, lamarin da ya kawo asarar kadarori masu yawa.

Duk da ba a rasa rai ba, Vanguard ta ruwaito yadda ganau ya tabbatar da tashin gobarar daga hawan karshe na otal din wurin karfe 7 na dare.

Ma'aikatan hukumar kashe gobara na jihar Legas suna ta kokarin kashe wutar.

A lokacin rubuta wannan rahoton, ba a tabbatar da abinda ya kawo gobarar ba duk da kuwa mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Amodu Shakiru ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Karin bayani na nan tafe...

Da duminsa: Gagarumar Gobara ta lashe fitaccen katafaren otal a Ikeja, Legas
Da duminsa: Gagarumar Gobara ta lashe fitaccen katafaren otal a Ikeja, Legas
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel