Abin kunya: Gwamnati ta na neman Shugaban Majalisar Kano a kan saba dokar COVID-19

Abin kunya: Gwamnati ta na neman Shugaban Majalisar Kano a kan saba dokar COVID-19

- Kwamitin gwamnatin tarayya na yaki da COVID-19 ta na neman Hamisu Chidari

- Shugaban majalisar dokokin Kano ya ki bari a killace shi bayan dawowa Najeriya

- Ana zargin Rt. Hon. Hamisu Chidari da amfani da takardun gwajin cuta na karya

Shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Rt. Hon. Hamisu Chidari, ya na cikin matafiya 200 da gwamnatin Najeriya ta buga kararrawa, ta ce ta na nemansu.

A wani rahoto na musamman da jaridar Premium Times ta fitar a ranar Litinin, ta ce ana zargin Hamisu Chidari da kin bin ka’idojin yaki da cutar Coronavirus.

A ranar 17 ga watan Mayu, 2021, Rt. Hon. Chidari ya dawo Najeriya ta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bayan ya yi aikin Umrah a kasa mai tsarki.

KU KARANTA: Tsofaffin Darektocin NSITF za su dawo da N180m da suka sata

‘Dan majalisar ya biyo jirgin saman Ethiopian airline, amma daga baya an gano cewa takardun da ya bada domin nuna bai dauke da cutar Coronavirus, na bogi ne.

Ana ganin cewa Chidari ya yi abin kunya a matsayinsa na shugaban majalisar dokoki na jihar Kano.

Da Honarabul Chidari ya iso filin jirgin sama, sai aka kai shi zuwa cibiyar National Women Development Centre tare da wasu sa'o'insa, inda aka shirya killace su.

A doka, ya kamata wadannan mutane da suka shigo Najeriya su kebe na kwanaki bakwai, kafin su samu damar shiga cikin sauran jama’a, saboda gudun yada ciwon.

Gwamnatin Najeriya ta na neman Shugaban Majalisar Kano kan saba dokar COVID-19
Hamisu Ibrahim Chidari Hoto: www.kanoassembly.gov.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: DSS ta fito da Shehin Malamin addini da ya yi shekaru 9 a daure

Bayan isowarsu ne sai shugaban majalisar ya ce bai gamsu da wannan wuri ba, ya zabi a kyale shi ya killace kansa a katafaren otel dinnan da ake kira Nicon Luxury.

A karshe Chidari ya ci amanar hukuma, ya sulale ba tare da ya killace kansa yadda ya yi alkawari ba.

Tun kafin nan jaridar ta ce Honarabul Chidari mai lambar fasfo B50022050, shi ne na 66 a cikin jerin mutanen da kwamitin SGF, Boss Mustapha ta ce ta na nema.

Kafin yanzu, kun samu rahoto 'Yan Majalisar Dattawa sun fadawa Gwamnoni, su bar maganar kara farashin fetur kamar yadda kwamitin NGF ya bada shawara.

Majalisa ta sha banban da Gwamnonin Jihohi, ba ta goyon bayan yin karin kudi a kan litar fetur. Gershom Bassey ya fadawa Gwamnati ta rika tausayawa Talakawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel