Jami’an tsaro sun saki Malamin Musulunci bayan ya shafe shekaru 9 a cikin ragar DSS
- Bayan shekaru kusan 10 a tsare, Abdullahi Mustapha Berende, ya samu ‘yanci
- Sheikh Abdullahi Berende ya na tsare a hannun jami’an DSS tun shekarar 2012
- An zargi Malamin da alaka da ‘Yan ta’adda da yi wa Iran leken asiri a Najeriya
Wani malamin addinin musulunci, Malam Abdullahi Mustapha Berende, da aka daure bisa laifin alaka da ‘yan kungiyar Al-Qaeda ya samu ‘yanci.
Daily Trust ta rahoto cewa Abdullahi Mustapha Berende wanda jami’an hukumar DSS masu fararen kaya su ka cafke tun 2012, ya dawo gida.
Jaridar ta ce an yi ram da Shehin ne shekaru tara da suka wuce bisa zarginsa da alaka da ‘yan ta’adda.
KU KARANTA: Babagana Kingibe ya zama Jakadan Najeriya a yankin Chadi
Abdullahi Mustapha Berende fitaccen malami ne kuma mai yin wa’azi a garin Ilorin, jihar Kwara, bayan shekaru tara a tsare, ya dawo gaban iyalansa.
Sheikh Mustapha Berende ya iso garin Ilorin ne a karshen makon da ya gabata tare da iyalinsa. Bayan ya iso gidansa, an shirya biki na dawowarsa.
Jama’a sun gudanar da addu’o’i na musamman a gidan dangin shehin malamin da ke garin Idi-Ape a karamar hukumar Ilorin ta gabas, jihar Kwara.
Abokan arziki da ‘yanuwa sun halarci wannan biki domin suyi murnar fitowarsa daga hannun hukuma.
KU KARANTA: Ni ban taba auren wata Aljana ba - Mijin Aljana
A shekarun da ya yi a tsare, Alkalan kotu da dama sun bada umarnin a fito da shi, amma duk da haka jami’an hukumar DSS suka cigaba da tsare shi har bana.
A yayin da wannan Bawan Allah yake tsare, ya sha da kyar a lokacin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi yunkurin ficewa daga gidan yari da ke Asokoro.
Wani ‘Dan uwan Malamin, Yakubu Berende, ya ji dadin sake ganin shehin. Jami’an tsaro sun yi ikirarin Sheikh Berende ya na yi wa kasar Iran aikin leken asiri.
Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma ya na ganin cewa babu ruwan 'yan kungiyar IPOB da kisan tsohon Hadimin shugaban kasa, Ahmad Gulak, a Owerri.
Gwamna Hope Uzodinma ya ce da ya ji an harbe Gulak a Owerri, bai iya zuwa coci ba. Gwamnan ya yi alkawarin cewa Gwamnati za ta yi bincike a kan lamarin.
Asali: Legit.ng