Sanatoci sun ja-kunnen Kwamitin Gwamna El-Rufai a kan bada shawarar kara kudin fetur

Sanatoci sun ja-kunnen Kwamitin Gwamna El-Rufai a kan bada shawarar kara kudin fetur

- Majalisar Dattawa ta na ganin karin kudin litar man fetur ba daidai ba ne

- Shugaban kwamitin FERMA, Sanata Gershom Bassey, ya bayyana wannan

- Gershom Bassey ya fadawa Gwamnati ta rika jin kan Talakawan Najeriya

Shugaban kwamitin majalisar dattawa da ke kula da hukumar FERMA mai alhakin gyara hanyoyi a kasa, Gershom Bassey, ya maida wa NGF martani.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa Sanata Gershom Bassey da kwamitinsa ba su goyon bayan kiran da kungiyar NGF ta ke yi na kara farashin man fetur.

Majalisar dattawa a karkashin Sanata Gershom Bassey ta ja-kunnen kungiyar gwamnonin jihohi da Nasir El-Rufai yake jagoranta a kan tada kudin man fetur.

KU KARANTA: Giyar mulki ce ke bugar da Gwamnan Kaduna - NUPENG

A wata hira da Gershom Bassey ya yi da ‘yan jarida a garin Abuja, ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da na tarayya su bi batun tsaida farashin fetur a hankali.

Gershom Bassey mai wakiltar Kudancin jihar Kuros Ribas a majalisar dattawan Najeriya ya ce al’umma suna cikin matsin tattali saboda rugujewar Naira.

“Akwai wasu abubuwa a game da sha’anin man fetur wanda kamfanin mai na kasa watau NNPC ya dade ya na magana a kansu.” Inji Sanatan na jihar Kuro Riba.

“Ina ganin ko menene ake magana a kai, ya kamata a sa tausayi wajen tsaida farashin kayan mai.”

Sanatoci sun ja-kunnen Kwamitin Gwamna El-Rufai a kan bada shawarar kara kudin fetur
Sanata Gershom Bassey Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Lafta haraji ne mafita a Najeriya - Gwamna El-Rufai

“Mu a halin yanzu, darajar Naira tana ta kara yin kasa, babu wani abin-a-yaba a game da kudin da mutane suke samu, amma ana maganar kara kudin fetur.”

Ya ce: “Ina tunanin ya kamata gwamnoni su sa rigar mutunci da tausayi wajen duban lamarin.”

Idan an yi karin farashi, kwamitin Nasir El-Rufai ya ba gwamnatin tarayya shawarar ta tanadi motocin haya da za su rika dawainiyar zirga-zirga cikin sauki.

Kwanakin baya kun samu labari cewa kwamitin NGF a karkashin gwamna Nasir El-Rufai ya bada shawarar a tsaida farashin litar fetur a kan N385-N408

Gwamna Nasir El-Rufai ya yi wannan bayani ne a wajen taron kungiyar gwamnonin Najeriya na NGF wanda aka yi ta kafar yanar gizo a cikin watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel