Koci 3 da za su iya karbar aikin Real Madrid bayan Zinedine Zidane ya ce zai tashi

Koci 3 da za su iya karbar aikin Real Madrid bayan Zinedine Zidane ya ce zai tashi

A ranar Laraba, 26 ga watan Mayu, 2021, jaridar Marca ta rahoto cewa Zinedine Zidane ya yanke shawarar zai tashi daga kungiyar kwallon Real Madrid.

Bisa dukkanin alamu, zaman kocin mai shekara 48 na biyu a kungiyar Real Madrid ya zo karshe bayan ya kashe gasar La-liga da Supercopa de Espana.

Shahararren ‘dan jaridar nan, Fabrizio Romano, ya tabbatar da cewa kocin zai bar kungiyar Real ne bayan ya gagara cin wani kofi a kakar shekarar bana.

Tun ba yau ba, mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafan na Sifen ya nuna zai sawake wa kowa, hakan ya nuna kamar ya na shirin ban-kwana ne.

Zinedine Zidane ya dauki wannan matsaya ne a lokacin da ‘yan wasansa suke sa ran ba zai tashi ba.

KU KARANTA: Atletico ta lashe La-liga, Real ta zo na biyu a 2021

A cikin makon nan ‘dan wasan kasar Jamus, kuma mai buga wa Real Madrid tsakiya, Toni Kroos, ya ce da a ce Zidane zai canza-sheka, da ya samu labari.

Spectator Index ta tabbatar da wannan rahoto a shafinta na Twitter, ta ce Zidane ya zabi ya ajiye aikinsa na babban mai horas da ‘yan kwallon Real Madrid.

An soma jita-jita a kan wadanda za su gaji Zinedine Zidane a Madrid. Daga ciki akwai;

1. Massimiliano Allegri

2. Raul Gonzales

3. Antonio Conte

Koci 3 da za su iya karbar aikin Real Madrid bayan Zinedine Zidane ya tashi
Massimiliano Allegri, Raul Gonzales da Antonio Conte Hoto: www.marca.com/en/football/real-madrid/2021/05/27/60aed5f2ca47419e478b468c.html
Asali: UGC

KU KARANTA: Jose Mourinho ya samu aiki bayan an kore shi daga Tottenham

Massimiliano Allegri tsohon kocin kungiyar AC Milan da Juventus ne wanda ya taka rawar gani a kasar Italiya. A halin yanzu ya na kasuwa, bai da aikin yi.

A jiya Antonio Conte ya zama bai da sana’a bayan barin Inter Milan. Kocin zai tashi ne kwanaki kadan bayan ya kai su ga lashe Seria A na farko tun 2010.

Bayan Massimiliano Allegri da Antonio Conte, sai Raul wanda kamar Zidane, tsohon ‘dan kwallon Real Madrid ne, yanzu ya na horas da Real Madrid Castilla.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng