Buhari ya yi fatali da kudirori fiye da 200 da ‘Yan Majalisar Dattawa suka aiko masa a shekaru 6

Buhari ya yi fatali da kudirori fiye da 200 da ‘Yan Majalisar Dattawa suka aiko masa a shekaru 6

- Shugaban kasa ya jefar da tulin kudirori da ‘Yan Majalisa suka aiko masa

- Akwai kudirorin Majalisar Dattawa da ake sauraron ya rattaba masu hannu

- Sai Buhari ya sa hannu, sannan kan Majalisa ta hadu kafin su zama dokoki

Akalla kudirori 40 daga cikin 49 da majalisar tarayya ta aika wa shugaban kasa a karkashin Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamilla sun makale a hanya.

Jaridar Punch ta ce kudirorin ‘yan majalisar suna sauraron i’itifakin juna ko amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin su zama dokokin kasa.

Wannan bincike na musamman da jaridar ta yi, ya nuna cewa a baya, shugaban kasa bai amince da kudirori 160 da majalisar Bukola Saraki ta aika masa ba.

KU KARANTA: Gwamna ya yi zazzaga, ya kori kusan duka Hadimai da Masu bada shawara

Rahoton ya ce daga cikin kudirori 287 da ‘yan majalisa suka zauna a kansu tsakanin 2015 zuwa 2019, kudirori 127 ne kacal suka samu shiga a fadar Aso Villa.

Daga lokacin da aka kafa majalisa mai-ci zuwa yanzu, an kawo kudirori 717, wanda yanzu 130 suna gaban kwamitoci, 43 sun kai matakin sauraron farko.

An karanto 370 daga cikin wadannan kudirori a karon farko a zauren majalisar dattawa. Ana kuma sa ran a saurari kudirori 126, sannan an amince da 48.

Abin da yake tsaida kudirorin Sanatocin shi ne jiran ‘yan majalisar wakilai su amince da su, ko kuma shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kai.

KU KARANTA: Ubangiji ya nuna mani tsohon Gwamnan Legas zai zama Shugaban kasa – Fasto

Buhari ya yi fatali da kudirori fiye da 200 da ‘Yan Majalisar Dattawa suka aiko masa a shekaru 6
Buhari da Shugabannin Majalisa Hoto: www.dailypost.ng
Asali: UGC

Daga cikin wadannan kudirori da ke teburin shugaban kasa akwai wadanda za su bunkasa tattali, kawo gyara a harkar rabon rijiyoyin mai, gyara aikin ‘yan sanda.

Manyan kudirorin Sanatocin da suke hannun kwamiti sun hada da na PIB da na gyara sha’anin zabe kamar yadda jaridar Vanguard ta fitar da rahoto kafin yanzu.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Babajide Omoworare, ya ce an yi watsi da kudirorin ne saboda sun ci karo da dokokin kasa.

Ya ce: “Shugaban kasa yana bada dalilin kin karbar kudiri. Wasu ayyukan da ake so kudirorin su kawo, suna karkashin wasu ma’aikatu, babu bukatar ayi mai-mai.”

Kwanaki baya an ji cewa majalisar wakilai ta aika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari gayyata, daga baya sai aka ji Sanatocin sun nisanta kansu daga batun.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, ya ce hakan ya saɓawa kundin dokar kasa sannan kuma ya sauka daga turba da tsarin aikin majalisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel