Bidiyo da hotunan tsuleliyar budurwa 'yar Najeriya da ta fara tuka jirgin sama a shekaru 17
- Wata budurwa 'yar Najeriya mai suna Maira Bashir El-Kanemi ta zama zakakura a fannin tukin jirgi
- Matashiyar budurwar ta fara tuka jirgin sama tun tana da shekaru 17 a duniya
- Bayan shekara daya, ta kware inda ta zama cikakkiyar matukiyar jirgin sama
Maira Bashir El-Kanemi budurwa ce matashiya 'yar Najeriya wacce tun asalinta take sha'awa tare da fatan tukin jirgin sama.
Matashiyar 'yar Najeriyan ta zama abun kwatance a kafafen sada zumunta bayan da wannan burin nata ya cika a kananan shekarunta.
KU KARANTA: Da duminsa: Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban sojin kasa
Maira kamar yadda Arewa Facts Zone a Twitter ta wallafa, ta fara tuka jirgin sama yayin da take da shekaru 17 a duniya.
'Yar asalin jihar Bornon bata tsaya a nan ba sai da ta karanci fannin tukin jirgi kuma ta zama cikakkiyar matukiyar jirgin sama yayin da take da ashekaru 18.
Matashiyar budurwar na fatan wata rana ta zama matukiyar jirgin sama na haya wata rana.
KU KARANTA: Muhimman abubuwa 6 da ya dace a sani game da Manjo Janar F Yahaya, sabon COAS
Wani ma'aboci amfani da Twitter mai suna @OvieAli ya wallafa bidiyon budurwar yayin da take tuka jirgin sama.
'Yan Najeriya sun yi martani ga wannan daukaka da matashiyar budurwar ta samu.
Wani @DavidKahleed cewa yayi: "Mutumiyar kirki ce fa, a duk inda ta ganka sai ta gaisheka. Koda kuwa baka ganta ba sai ta kira ka sannan ta gaisheka... Ta kan baiwa mahaifiyata kyautar kudi. Allah yayi miki albarka. Zan adana wannan bidiyon in nuna mata idan muka hadu in nuna mata."
@abdul_mairabo ya rubuta: "Allah ya cigaba da bata sa'a!."
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Basheer Mohammed a matsayin sabon darakta janar na hukumar yaki tare da hana safarar mutane (NAPTIP).
Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya sanar da hakan a wata wallafa da yayi a ranar Alhamis a shafinsa na Twitter.
Shehu yace shugaban kasan ya amince da wasu manyan sauye-sauye a ma'aikatar tallafi da jin kai tare da walwalar 'yan kasa.
Asali: Legit.ng