2023: Fasto ya fadi shahararren Jigon APC da zai gaji Buhari a kan kujerar Shugaban kasa
- Bishof Ayodeji Ipinmoroti ya ce Bola Tinubu zai yi nasara a zaben 2023
- Ayodeji Ipinmoroti ya fadawa Tinubu ya yi takara idan yana neman mulki
- Faston ya bayyana cewa wasu na-kusa da ‘Dan siyasar za su ci amanarsa
Babban limamin cocin Christ Revelation Church of God da aka fi sani da Holy Promise, Ayodeji Ipinmoroti, ya fadi wanda zai zama shugaban kasa a 2023.
The Nation ta rahoto Bishof Ayodeji Ipinmoroti ya na cewa Ubangiji bai tsara Najeriya ta yadda za ta wargaje ba, ya kuma fadi wanda zai hana kasar barkewa.
Ayodeji Ipinmoroti ya yi wannan bayani ne wajen murnar zuwan ranar yara wanda ake yi a ranar 27 ga watan Mayu, inda ya tabo magana kan zabe mai zuwa.
KU KARANTA: Gwamnatin APC ba ta tsinana komai ba a shekara 6 - Masu karatu
Bishof Ipinmoroti yake cewa Ubangiji ya nuna masa tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu zai zama shugaban kasa bayan Muhammadu Buhari.
Limamin na cocin Holy Promise ya ce amma dole sai an kauda wasu abubuwa kafin Asiwaju Bola Tinubu ya iya dare wa kan kujerar shugaban kasar Najeriya.
Ya ce: "Tinubu zai yi nasarar zama shugaban kasa, duk da wasu na kusa da shi za su yaudare shi kafin zabe," ya ce shi ne zai iya dinke barakar da ake fama da ita.
PM News ta rahoto shi ya ce: “Tsarin Najeriya zai dawo daidai, amma sai mun tuba daga zunubanmu. Ana bukatar addu’o’in masu imani kafin abubuwa su mike.”
KU KARANTA: Gwamnati za ta gina gidajen da za a rabawa mutane miliyan 1.5
Bishof Ayodeji Ipinmoroti ya ce: “Ba na ganin Najeriya za ta barke. Bola Tinubu shi ne wanda ya fi dace wa da tsaya wa takarar shugaban kasa a zaben me zuwa.”
“Mutum ne mai daraja, wanda ya san kan aiki da kwarewa a harkar siyasa har ya kai ga ci a kasa.” Shehin ya ce Tinubu ya shiga harama idan ya na son shugabanci.
“Ni malami ne kuma limami. Ubangiji ya aiko ni ga Tinubu. Idan mu ka yi ido-biyu, zan fada masa abin da na-gani, na ga za a yaudare shi, amma zai samu mulki.”
A ranar da aka sace yara a jihar Neja, Shehu Sani ya ce an yi garkuwa da wani ‘Dan Majalisar jihar Nasarawa a hanyarsa ta zuwa garin Kaduna daga Akwanga.
Sanata Shehu Sani ya ce okaci ya yi da Gwamnati za ta gano Miyagun da suka addabin Bayin Allah, suke kashe-kashe, suna awon-gaba da mutane a Arewa.
Asali: Legit.ng