Masu karanta shafin Legit Hausa sun ce Buhari bai cika duka alkawuran da ya dauka a 2015 ba

Masu karanta shafin Legit Hausa sun ce Buhari bai cika duka alkawuran da ya dauka a 2015 ba

- Gwamnatin APC ta cika shekara 6 a karagar mulkin Najeriya a karshen makon jiya

- Masu karanta shafin Legit.ng Hausa sun fada mana ra’ayinsu game da wannan mulki

Da muka tambayi masu karanta shafin Legit.ng Hausa a Twitter game da rawar ganin gwamnatin APC, sun nuna kamar ba su gamsu da tafiyar ba.

A ranar 29 ga watan Mayu, 2021, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta cika shekaru shida a kan mulki, bayan rantsar da ita a Mayun 2015.

Mafi yawan wadanda suka amsa wannan tambaya, su na ganin kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba tukun.

KU KARANTA: Buhari ya yi magana a kan karya darajar Naira

A halin yanzu, gwamnatin tarayya ta na da shekaru biyu a wa’adinta, bayan nan za a sake yin zabe domin a mika ragamar mulki ga wasu na-dabam.

Mun jefa wannan tambaya a dandalin Twitter, mu ka ce: “A jerin manyan alkawuran da Gwamnatin APC ta dauka, shin wanne kuke ganin @MBuhari ya cika daga 2015 zuwa yau: Inganta tsaro, yaki da rashin gaskiya, habaka tattalin arziki, ko kuma babu ko daya?

A ranar Asabar ne mu ka yi wannan tambaya, mu ka bar kofar a bude, inda sai zuwa ranar Lahadi, 30 ga watan Mayu, 2021, masu bibiyarmu suka gama amsa wa.

Kashi 16.7% sun ce a mulkin APC, an inganta tsaro a cikin shekaru shidan nan da suka wuce. A wannan bangare ne gwamnatin ta fi samun kuri’a masu tsoka.

KU KARANTA: Buhari ya yi martani bayan an bindige Hadimin Jonathan

Masu karanta shafin Legit Hausa sun ce Shugaba Buhari bai cika duka alkawura 3 da ya dauka ba
Shugaba Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Sai kuma 4.8% suka ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika alkawarin da ya dauka na cewa gwamnatinsa za ta yi yaki da rashin gaskiya ba tare da son kai ba.

A ra’ayin 6% daga cikin makarantanmu da suka amsa wannan tambaya, sun ce an bunkasa tattali.

72.6% sun ce a cikin wadannan manyan alkawura, ba a cika ko daya ba. Wadannan kaso ne suka fi samun kuri’a, kusan ¾ na masu bibiyarmu suna kan wannan ra’ayi.

A yau aka ji cewa hukumar gwamnatin Muhammadu Buhari za ta sa kafar wando daya da duk wadanda suka karbi bashin kudi, suka yi gaba ba tare da sun biya ba.

Hukumar AMCON ta ce wasu mutum 350 a Najeriya su ka ci bashin N3.5tr, har yau sun ki biyan kudin, don haka ne ake shirin gurfanar da su a gaban kotu a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng