An Rufe Makarantar Sakandare Ta Mata Saboda Tsoron 'Iskokai' a Kwara

An Rufe Makarantar Sakandare Ta Mata Saboda Tsoron 'Iskokai' a Kwara

- An rufe makarantar sakandare ta mata ta St Claire's Girls Grammar School, Offa, jihar Kwara

- Hakan na zuwa ne bayan daliban makarantar sun shiga firgici kan abin da suka kira muryar 'iskokai' a makarantar

- Daya daga cikin jami'ar makarantar ta ce irin wannan mummunan lamarin ya taba faruwa lokacin tana daliba a 1978

Mahukunta a Makarantar Sakandare ta Mata na St Claire's Girls Grammar School, Offa, jihar Kwara sun rufe makarantar saboda firgici kan jin wasu muryoyi da ake zargin 'iskokai' ne a makarantar, The Nation ta ruwaito.

Bayannan da aka tattaro sun nuna cewa mahukunta a makarantar sun umurci iyaye da masu kula da yara su tafi da yaransu gidajensu.

An Rufe Makarantar Sakandare Ta Mata Saboda Tsoron 'Iskokai' a Kwara
An Rufe Makarantar Sakandare Ta Mata Saboda Tsoron 'Iskokai' a Kwara. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Nigeria Ba Za Ta Taɓa Zama Ƙasar Musulunci Ba, In Ji Jikan Shagari

Majiyar Legit.ng ta gano cewa afkuwar wannan lamarin mai daure kai ya janyo fargaba a tsakanin dalibai har ma da malamai a makarantar.

Lamarin mai ban mamaki ya faru ne a ranar Juma'a a wannan makon a yayin da wasu dalibai suka rika ihu bayan jin wasu muryoyi masu daure kai da ake zargin na 'iskokai' ne.

Daliban da suka tsorata sun fice da ajijuwansu da dakunan kwanansu kamar yadda rahoto ya nuna.

Da ya ke tabbatar da lamarin, kakakin hukumar tsaro ta NSCDC na jihar Kwara, Babawale Afolabi, ya ce, "daliban suna ta ihu a harabar makarantar bayan jin wani murya da suke zargin ta fita daban da abin da suka saba ji."

KU KARANTA: Direban Babban Mota Ya Halaka Jami'in FRSC a Jihar Kano

Ya kara da cewa, "Da muka tuntube su, daya daga cikin mahukunta a makarantar, ta sanar da mu cewa abin ya bawa jami'an makarantar mamaki, tana mai cewa irin wannan mummunan abin ya tafa faruwa a lokacin tana daliba a makarantar a 1978.

"Wata daliba, wacce abin ya faru da ita ta ce ta ga wasu mata sanye da tufafi masu launi daban-daban suna kiranta amma bata amsa ba a yayin da suke son janyo ta da karfi da yaji. Hakan yasa ta tsaga ihu ta kuma fadi kasa sumammiya."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel