An Yi Gumurzu Tsakanin Sojoji Da Mayaƙan Boko Haram a Diffa

An Yi Gumurzu Tsakanin Sojoji Da Mayaƙan Boko Haram a Diffa

- Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari birnin Diffa da ke Jamhuriyar Nijar

- Sojoji da jami'an tsaro a kasar sun yi musayar wuta da yan ta'addan sai dai ba a san adadin wadanda suka mutu ba

- Majiyoyi daga Nijar sun tabbatar da harin sai dai daga bisani sun ce an samu lafiya a garin bayan sojoji sun fatattake yan ta'addan

Mummunan fada ta barke, a ranar Juma'a, tsakanin dakarun sojoji da mayakan Boko Haram a Diffa, kudu maso gabashin Nijar, a cewar hukumomin kasar, ba tare da bada cikaken bayani kan wadanda suka mutu ba, The Channels ta ruwaito.

Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a Diffa, wanda ke kusa da iyakar Nigeria, daga kuduncin misalin karfe 3 - 4 na yamma, babban jami'i a kasar ya shaidawa AFP.

'Yan Boko Haram Sun Kai Hari Birnin Diffa a Jamhuriyar Nijar
'Yan Boko Haram Sun Kai Hari Birnin Diffa a Jamhuriyar Nijar. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu Zanga-Zanga Sun Tafi Da Gawarwaki Zuwa Fadar Sarkin Zurmi a Zamfara

"Jami'an tsaro da sojoji sun mayar da wuta ciki har da amfani da manyan makamai," majiyar ta kara da cewa.

Wata majiya ta biyu ta tabbatar da afkuwar harin amma itama ba ta bada cikakken bayani ba.

"Ba mu san adadin wadanda suka mutu ba, amma sun ga mutane suna ta tserewa saboda firgici," majiyar ta ce kafin kara cewa a yanzu lamaru sun daidaita a birnin mai mutane kimanin 200,000.

KU KARANTA: Direban Babban Mota Ya Halaka Jami'in FRSC a Jihar Kano

An sha kaiwa Diffa hari lokuta da dama tun 2015. A mayun 2020, mummunan fada ya barke tsakanin sojoji da masu ikirarin jihadi a gadar Doutchi da ta hada Nigeria da Jamhuriyar Nijar.

Fada da yan Boko Haram da ISWAP ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 36,000 tun 2019 kuma ya saka kimanin mutane miliyan biyu barin gidajensu.

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164