Hotunan Samamen Da Sojoji Suka Kai Mabuyar Ƴan Aiken Ƴan Boko Haram

Hotunan Samamen Da Sojoji Suka Kai Mabuyar Ƴan Aiken Ƴan Boko Haram

- Sojojin Nigeria sun kama wasu da ake zargin yan sakon yan kungiyar Boko Haram ne

- An kama wadanda ake zargin ne yayin da sojoji suka kai samame sansanin yan sakon Boko Haram a Gujba a ranar Asabar 29 ga watan Mayu

- Mai magana da yawun rundunar sojojin Nigeria, Birgediya Janar Yerima ya tabbatar da sumamen da kamen

Rundunar sojojin Nigeria na cigaba da samun nasara a kan yan ta'addan kungiyar Boko Haram a yayin da suke ragargazar su a yankin arewa maso gabashin kasar.

Dakaru sojojin Operation Hadin Kai sun kama wasu mutane biyu da ake zargin yan sakon yan Boko Haram ne a Gujba a jihar Yobe.

Hotunan Samamen Da Sojoji Suka Kai Mabuyar 'Yan Sakon Boko Haram
Hotunan Samamen Da Sojoji Suka Kai Mabuyar 'Yan Sakon Boko Haram. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An Yi Gumurzu Tsakanin Sojoji Da Mayaƙan Boko Haram a Diffa

Birgediya Janar Mohammed Yerima, direktan sashin watsa labarai na rundunar sojoji ya tabbatar da hakan inda ya ce sojojin sun kama mutane biyu da ake zargin yan sakon yan ta'addan ne a ranar 29 ga watan Mayu bayan kai samame a mabuyarsu.

Yerima cikin sanarwar da ya wallafa a shafin sojoji na Facebook da Twitter ya ce an yi nasara a sumamen an kuma damke wadanda ake zargin.

Kayayyakin da aka samu a hannun wadanda ake zargin sun hada da jarkoki 11 makare da man fetur, jarkoki 6 makare da man gas da jarkoki 9 da aka boye a wurare daban-daban.

KU KARANTA: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Umahi Ya Sauke Masu Riƙe da Muƙaman Siyasa a Jiharsa

Ya ce a halin yanzu wadanda ake zargin suna hannunsu sannan nan gaba za a mika su ga hukumomin da suka dace domin a hukunta su bayan kammala bincike.

A wani labari daban, a kalla mutane 10 ne suka gamu da ajalinsu a hannun yan bindiga yayin hari da harin ramuwar gayya da suka kai a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a cewar rahoton TVC News.

A cewar kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, yan bindigan sun kai hari kauyen Na'ikko a karamar hukumar Giwa inda suka yi musayar wuta da wasu yan garin hakan ya yi sanadin mutuwar mutane uku yan garin.

Mr Aruwan ya ce matasan kauyen Na'ikko sun mayar da martani ta hanyar kai hari Rugan Abdulmuminu, wani rugar fulani da ke kusa da su, inda suka kashe mutum biyu da ake zargin sun kai harin farkon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel