Da duminsa: Jam'iyyar APC ta sha mumunar kaye a kotun kolin Najeriya

Da duminsa: Jam'iyyar APC ta sha mumunar kaye a kotun kolin Najeriya

- Jam'iyyar APC ta sha kaye a karar da take sa ran tunbuke gwamna Godwin Obaseki na Edo da shi

- Alkalan kotun koli sun yi ittifaki kan watsi da kara saboda rashin isassun hujjoji

- Yanzu dai kotun koli ta raba gardama na karshe kan wannan lamari

Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar zargin amfani da takardan karatu na bogi da All Progressives Congress (APC) ta shigar kan gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

A ranar Juma'a, 28 ga Mayu, kotun kolin ta yanke cewa APC da mambanta, Williams Edobor, sun gaza gabatar da isassun hujjoji kan tuhumar da suke yiwa gwamnan jihar Edo, rahoton Vanguard.

A riwayar TheNation, kwamitin Alkalai biyar sun yi ittifaki wajen watsi da karar.

Kotun ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara wacce ta amince da hukumar babban kotun Najeriya a ranar 9 ga Junairu, 2021.

Babbar kotun ta tabbatar da sihhancin kwalin digirin Obaseki wacce jami'ar Ibadan UI ta basa.

DUBA NAN: Nan da shekara 2, har yan adawa sai sun jinjinawa shugaba Buhari: Fadar Shugaban kasa

Da duminsa: Jam'iyyar APC ta sha mumunar kaye a kotun kolin Najeriya
Da duminsa: Jam'iyyar APC ta sha mumunar kaye a kotun kolin Najeriya
Asali: UGC

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

A bangare guda, fadar shugaban kasa, a ranar Juma'a, ta bayyana cewa kafin karewar wa'adin shugaba Muhammadu Buhari a 2023, ko masu adawa sai sun jinjinawa masa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin murnar cikar Buhari shekaru 6 kan mulki.

Adesina ya lissafa jerin nasarori da ayyukan da shugaba Muhammadu Buhari yayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel