Muhimman abubuwa 6 da ya dace a sani game da Manjo Janar F Yahaya, sabon COAS

Muhimman abubuwa 6 da ya dace a sani game da Manjo Janar F Yahaya, sabon COAS

- Farouk Yahaya sojan Najerya mai mukamin Manjo Janar wanda ya fito daga jihar Sokoto dake arewa maso yammacin kasar nan

- Sabon shugaban hafsin sojin Najeriyan ya halarci makarantar horar da hafsin sojoji inda ya kammala a aji na 37

- Kafin nadinsa, shine mai baiwa rundunar Operation Hadin Kai umarni dake yankin arewa maso gabas

A yau 27 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Yahaya Farouk a matsayin shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya.

Idan zamu tuna, tsohon shugaban hafsin sojin kasa, Marigayi Laftanal Janar Ibrahim Attahiru ya rasu sakamakon hatsarin jrigin sama tare da wasu jami'ai 10 a ranar Juma'a 21 ga watan Mayu.

An birnesu bayan jana'izar da aka yi musu a ranar Asabar 22 ga watan Mayu a Abuja inda wasu ministoci da gwamnoni suka samu damar hallara.

KU KARANTA: Nasara daga Allah: 'Yan sanda da 'yan sa kai sun sheke 'yan bindiga 10 a Zamfara

Muhimman abubuwa 6 da ya dace a sani game da Manjo Janar F Yahaya, sabon COAS
Muhimman abubuwa 6 da ya dace a sani game da Manjo Janar F Yahaya, sabon COAS. Hoto daga @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Nadin Farouk Yahaya ya bazu ne bayan sanarwar da mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya wallafa a shafin hedkwatar na Twitter.

Ga muhimman abubuwa shida da ya dace a sani game da sabon shugaban dakarun sojin kasan:

1. Har zuwa yau da aka nada shi, Manjo janar Farouk Yahaya shine mai bada umarni ga rundunar Operation Hadin Kai wacce a da aka sani da Operation lafiya Dole a yankin arewa maso gabas.

2. Sabon shugaban hafsin sojin kasan dan asalin jihar Sokoto ne.

3. Yahaya ya halarci makarantar horar da hafsin soja dake Kaduna kuma ya kammala a aji na 37.

4. Shine tsohon babban jami'i mai bada umarni ga Div 1 dake rundunar sojin Najeriya.

5. Sabon shugaban hafsin sojin kasan ya karba ragamar cibiyar bincike ta rundunar sojin kasa daga hannun Manjo Janar Olusegun Adeniyi.

6. Shine mai bada umarni ga birged ta hudu ta rundunar sojin Najeriya.

KU KARANTA: Dakarun sojin Najeriya sun damke masu samarwa Boko Haram man fetur a Yobe

A wani labari na daban, fasinjoji masu tarin yawa sun nitse a yankin arewa maso yammacin Najeriya a ranar Laraba bayan tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Neja, jami'i mazaunin yankin ya tabbatar.

Jirgin ruwa da ya bar jihar Kebbi yana tunkarar yankin arewa maso yammacin jihar Kebbi ya fashe sannan ya nitse, Abdullahi Buhari Wara, hakimin Ngaski ya tabbatar.

"Tuni dai masu ceto suka fada kogin amma mutum 22 tare da gawar mutum daya suka iya tsamowa," Wara yace a yanzu kusan fasinjoji 140 ne babu duriyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel