Wata sabuwa: Bashin da ake bin Najeriya ya kara yawa

Wata sabuwa: Bashin da ake bin Najeriya ya kara yawa

Bashin kudin da ake bin Najeriya ya yi tashin gwauron zabi daga naira tiriliyan 3.32 zuwa naira tiriliyan 25.7 a cikin shekara daya, a cewar hukumar kula da bashi ta kasa (DMO) a ranar Talata.

Ana bin gwamnatin tarayya bashin naira tiriliyan 20.42 a ranar 30 ga watan Yuni, 2019 inda jihohi 36 da kuma gwamnatin tarayya ake binsu jimillar kudi har naira tiriliyan 5.28.

Jimillar bashin ya hada da naira tiriliyan 8.32 wacce take dai-dai da dala biliyan 27.16 bashin waje da kuma naira tiriliyan 17.38 bashin cikin gida kamar yadda DMO ta sanar.

Bashin kasar ya tsaya a naira tiriliyan 22.38 ne a watan Yuni, 2018 inda ya haura zuwa naira tiriliyan 24.39 a watan Disamba, 2018 kafin dagawarsa zuwa naira tiriliyan 24.95 a watan Maris, 2019.

DUBA WANNAN: Boko Haram: An binne sojoji 847 a iya makabartar sojoji ta Maiduguri - Sanata Ndume

A watan da ya gabata ne, kwamitin dokokin kudi na babban bankin Najeriya ya ce, hauhawar bashin kasar na daya daga cikin abinda ke watangarar da cigaban kasar.

A watan Augustan wannan shekarar ne ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce, bashin kasar nan ba kalubale bane gareta amma babban kalubalen kasar shine rashin samun isashen kudin shiga.

"Babu abin damuwa game da yawan bashinmu. Inaso in kara jaddada cewa, bashinmu bai yi yawa ba; babban kalubalenmu shine kudin shiga. Har yanzu bashinmu madaidaici ne. A takaice ma dai, a cikin kasashe tsararrakinmu, mu ke da mafi karancin bashi," a cewarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel