AGF Malami ya hana mu tattaro kudin da aka sace daga NNPC aka boye a kasar waje
- Ana zargin Ministan shari’a da kawo matsala wajen tattaro wasu kudin sata
- Tosin Ojaomo ya ce SPIPP ta bankado tulin kudin da aka wawura daga NNPC
- A karshe AGF ya sa aka ruguza SPIP, ya ce wannan ne ya sa komai ya bi ruwa
Babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami SAN, ya na fuskantar zargin yi wa gwamnati zagon-kasa.
Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto cewa wani babban lauya yana tuhumar Ministan da hana a karbo wasu kudi fam Dala biliyan 60 daga Amurka.
Tosin Ojaomo wanda lauya ne na musamman da ya yi aiki da kwamitin SPIP da shugaban kasa ya taba kafa wa, ya bayyana wannan a ranar Larabar nan.
KU KARANTA: Minista ya na taba kudin da aka karbo a wajen barayi inji Majalisa
Barista Tosin Ojaomo ya yi wannan bayani ne a gaban kwamitin da ke bincike a kan kadarorin da gwamnatin Najeriya ta karbo a hannun barayin gwamnati.
Ojaoma ya na cikin lauyoyin da su ka tsaya wa tsohon shugaban hukumar EFCC, Mista Ibrahim Magu a gaban kwamitin binciken da Ayo Salami ya jagoranta.
Mista Ojaomo bai gabatar da wata takarda ko wata hujja da za ta gaskata zargin da ya ke yi wa Abubakar Malami SAN ba, amma ya hakikance a kan bakarsa.
Jaridar Guardian ta ce duk da rashin hujjoji a kasa, shugaban kwamitin binciken, Honarabul Adejoro Adeogun, ya ba Lauyan damar ya cigaba da yin bayani.
KU KARANTA: Bamu goyon bayan aika-aikan Sojojin tawaye a kasar Mali – Najeriya
A cewarsa Ministan ya hana Special Presidential Investigation Panel for Recovery of Public Property karbo wasu kudi da aka sata daga asusun Najeriya.
Kamar yadda Lauyan ya bayyana, an wawuri Dala biliyan 60 a baitul-malin Najeriya daga NNPC, sannan aka boye wadannan kudi a Texas, birnin kasar Amurka.
Ya ce saura kiris a dawo da tiriliyoyin da aka dankare a bankin Amurka da wasu kudin da aka boye da sunnan NNPC a Najeriya, sai Ministan ya ruguza kwamitin.
Ku na da labarin cewa ‘Yan Majalisar tarayya sun sa danba, suna binciken kudi da duk kadarorin da hukumar EFCC ta karbe tun daga shekara 2002 har 2020
Da aka taso shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa a gaba da bincike, sai ya ce bai wuce kwana 100 da shiga ofis ba, bai gama sanin wasu abubuwan da su ka faru ba.
Asali: Legit.ng