Matsalar tsaro: ‘Dan Majalisar Tarayya ya kai korafi gaban Majalisa da fadar Shugaban kasa

Matsalar tsaro: ‘Dan Majalisar Tarayya ya kai korafi gaban Majalisa da fadar Shugaban kasa

- Muraina Ajibola ya ce mutanensa na cikin mummuna matsalar rashin tsaro

- ‘Dan majalisar ta kai korafi zuwa fadar Shugaban kasa da kwamitin majalisa

- Ajibola ya na so gwamnatin tarayya ta biya wadanda abin da ya shafa diyya

'Dan majalisar tarayya, Honarabul Muraina Ajibola mai wakiltar mazabar Ibarapa ta tsakiya da Ibarapa ta Arewa ya kai kara zuwa fadar shugaban kasa.

Leadership ta ce Muraina Ajibola ya kai kara gaban shugaban kasa da majalisar tarayya a kan yawan satar mutanen da ake yi a mazabarsa a jihar Oyo.

Honarabul Muraina Ajibola ya bukaci gwamnati ta biya wadanda matsalar rashin tsaro ta shafa diyya.

KU KARANTA: Biliyan nawa aka gano a hannun barayin gwamnati? – Sultan

‘Dan majalisar ya jero sunayen wadanda aka yi garkuwa da su a yankin Ibarapa. Muraina Ajibola ta kai jerin gaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai.

Ajibola ya gabatar da korafin a madadin sarakunan gargajiya, masu fada-a aji, shugabannin addini, matasa, mata, ‘dalibai, masana da manoman Ibarapa.

‘Dan siyasar ya ce an matsa wa yankin Igboora, Idere, Igangan, Tapa da Aiyete da kashe-kashe duk da cewa duk mutanen kauyukan masu karamin karfi ne.

A korafin, Ajibola, ya ce ya dade ya na koka wa majalisa ana addabar talakawanta, ana garkuwa da su, ayi masu fyade, sannan kuma ana karbe masu dukiya.

KU KARANTA: Babu yadda aka iya, tilas sai farashin fetur ya kara tsada – MAN

Matsalar tsaro: ‘Dan Majalisar Tarayya ya kai korafi gaban Majalisa da fadar Shugaban kasa
'Yan Majalisa Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Rahoton ya ce Hon. Muraina Ajibola ya nemi hukuma ya yi bincike, ya cafke wadanda su ke da laifin wannan danyen aiki, sannan a biya mutanen kudin diyya.

Da ya ke magana ta bakin hadiminsa, Olubunmi Sodipo, ‘dan majalisar ya ce a dalilin halin da ake ciki, mutanensa suna cikin kunci, ba su iya fita neman abinci.

Shugaban NDLEA mai yaki da safarar miyagun kwayoyi, Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya ce za a rika yi wa ‘Yan siyasa gwajin amfani da miyagun kwayoyi.

Hukumar NDLEA ta kawo shawarar a soma yi wa Dalibai gwajin shan kwaya kafin su samu damar yin karatu a manyan makarantun gaba da sakandare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng