Tsabar rashin imani ya sa Soja ya kashe wani Bawan Allah da ya ba shi gyaran hanya a mota

Tsabar rashin imani ya sa Soja ya kashe wani Bawan Allah da ya ba shi gyaran hanya a mota

- Wani mutum ya taimakawa Soja a titi, ya yi masa gyaran hanya a Ribas

- Kafin a kai inda za a sauka, jami’in Sojan ya kashe wannan Bawan Allah

- Ana zargin sojan ya jefar da gawarsa a jeji, sannan ya yi gaba da motarsa

Daily Trust ta ce wani jami’in soja da ke aiki da bataliya ta 6 da ke garin Akwa Ibom, ya shiga hannun hukuma bisa zarginsa da aikata laifin kisa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ana tuhumar wannan soja mai suna Stephen I. da laifin kashe wani mutumi da ya taimaka ya dauko sa a motarsa.

Marigayi Enobong Jimmy ya nemi ya ba wannan jami’in tsaro gyaran hanya daga garin Fatakwal a jihar Ribas zuwa Ikot Abasi da ke jihar Akwa Ibom.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun ba Makiyaya sharadin shigowa Kano

Sahara Reporters ta ce a karshe Stephen I ya yi sanadiyyar mutuwar wannan mutum, ya kashe shi kafin su isa, ana zargin ya harbe shi ne da bindiga.

Bayan sojan ya aika wannan mutumi barzahu, sai ya jefar da gawarsa a kan hanya, bayan haka ya yi gaba da motar marigayin, kafin a samu ayi ram da shi.

Majiyoyi sun shaida mana daga baya ‘yan sanda sun gano gawar Enobong Jimmy, suka ajiye a asibiti, sannan aka shiga binciken inda aka kai motarsa.

Jami’an ‘yan sanda sun gano motar marigayin ne a karamar hukumar Ukanafun da e Akwa Ibom.

KU KARANTA: Ana kashe mani mutane - 'Dan Majalisa

Rashin imani ya sa Soja ya kashe wani Bawan Allah da ya ba shi gyaran hanya a mota
Hoto: dailytrust.com / www.youtube.com
Asali: UGC

An yi nasarar gano inda aka kai motar ne bayan an yi amfani da na’urar da ke nuna inda mota ta ke. Daga nan, aka tsare wannan soja da ake zargi da kisan kai.

Bayan ‘yan sanda sun cafke wannan mutum, rundunar sojoji ta karbo shi da nufin ayi masa shari’a a gidan soja, domin sojoji suna da kotunsu na musamman.

Wani ‘dan uwan marigayin, ya ce ‘danuwansa ya mutu ya bar mata guda, da kananan ‘ya ‘ya biyu. Haka zalika, gidan soja ta ce tabbas wanda ake zargi jami’inta ne.

A ranar Laraba kun ji cewa miyagun ‘Yan bindiga sun daura miliyoyi a kan wasu Bayin Allah akalla 13 da suka yi garkuwa da su a wani kauye da ke jihar Neja.

‘Yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan 100 kafin jama’a su sake ganin ‘yanuwansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel