‘Yan bindiga sun bukaci a biya sama da N100m kafin a fito da mutane 13 da aka sace a Neja

‘Yan bindiga sun bukaci a biya sama da N100m kafin a fito da mutane 13 da aka sace a Neja

- Kwanakin baya aka yi garkuwa da wasu mutane 13 a Kauyen Kwakwashi

- ‘Yan bindiga sun tuntubi Iyalan wadannan Bayin Allah da ake tsare da su

- An bukaci ‘Yanuwa su lalo kudi kafin su sake hada ido da masoyan na su

‘Yan bindigan da su ka kai hari a kauyen Kwakwashi dake jihar Neja, sun hallaka wani mutum daya, sannan kuma sun yi awon-gaba da mutane 13.

Jaridar Punch ta ce wadannan miyagu sun tuntubi ‘yan uwan mutanen da suka dauke, kuma sun bukaci a biya kudi a matsayin fansa kafin su fito da su.

Wani dattijo da ke wannan gari na Kwakwashi, Alhaji Aliyu Muhammed, ya zanta da ‘yan jarida a karshen makon da ya gabata, inda ya tabbatar da haka.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun kama soja da zargin kashe wani 'dan kasuwa

Alhaji Aliyu Muhammed yake cewa an tuntubi iyalai da ‘yanuwan wadanda aka yi garkuwa da su, kuma an bayyana masu kudin fansar da ake so su biya.

A cewar wannan Bawan Allah, kudin da aka kayyadewa wadannan mutane da ke tsare sun banbamta.

Abin da aka bukaci ‘yanuwa da iyalan dukkaninsu su hada, ya haura Naira miliyan 100, kamar yadda ya shaida wa manema labarai da aka yi magana da shi.

“An nemi wani ya kawo N50m, an bukaci wani jami’in hukumar NSCDC ya nemo N17m, wasu mutane za su fito da N10m.” Aliyu ya ke fada ta wayar salula.

KU KARANTA: An kashe mutane a Zamfara, an yi gaba da wasu da yawa

‘Yan bindiga sun bukaci a biya sama da N100m kafin a fito da mutane 13 da aka sace a Neja
‘Yan bindiga sun shiga Neja Hoto: www.msn.com/en-xl/africa/nigeria
Asali: UGC

“Ba zan iya tuna adadin da aka nema daga hannuun kowane dangi ba, amma N10m ne mafi karancin abin da aka tambaya, sannan N50m abin da ya fi yawa.”

Dattijon ya kara da: “Yanuwan wadanda aka tsare suna neman yadda za su samu wadannan kudi bayan ‘yan bindigan sun hakikance a kan adadin da suka bukata.”

Ana sa rai idan wadannan miyagun mutane sun sake kira a waya, su rage kudin fansar da su ka sa. MSN Africa ta tabbatar da wannan rahoto a ranar Litinin dinnan.

Wani rahoto da SBM Intelligence ta fitar ya tabbatar da cewa daga farkon shekarar 2021 zuwa yau, Boko Haram ta kai hare-hare sama da 100 a jihohi hudu na Arewa.

Hakan ya na nufin a duk rana ta Duniya, sai mutum 6 sun gamu da ta’adin Boko Haram a kwanaki 140. A dalilin hakan, an jikkata mutane sama da 900 kawo yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng