Majalisa ta tatse sabon Shugaban EFCC a kan abubuwan da suka faru har a lokacin Magu
- Majalisa ta dauko binciken kadarorin da EFCC ta karbe daga 2002 zuwa 2020
- Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ya bayyana a gaban kwamitin binciken
- Abdulrasheed Bawa ya gaza yin bayani kan wasu kudi da aka cire tun a 2017
Wani kwamitin majalisar wakilan tarayya da ke binciken kudin da EFCC ta karbo daga hannun masu zagon-kasa, ta zauna da Abdulrasheed Bawa.
Daily Trust ta ce ‘yan majalisa sun zauna da shugaban hukumar EFCC domin gano gaskiyar kadarorin da aka karbe daga shekarar 2002 zuwa 2020.
A ranar Laraba, kwamitin majalisar ya zauna da shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa.
KU KARANTA: Jerin wadanda suka rike mukamin shugaban hukumar EFCC
Kamar yadda Premium Times ta fitar da rahoto, a zaman yau, an tado da batun wasu abubuwa da suka faru tun a lokacin da Ibrahim Magu yake rike da EFCC.
Da yake bayani kwanaki, Abdulrasheed Bawa ya yi ikirarin cewa babu ko sisin kobo da hukumar EFCC ta taba daga cikin asusun da ake tattara kudin sata.
Amma da kwamitin yake bincike, Hon. Darlington Nwakocha, ya gano wasu kudi da EFCC ta tura wa asusun Africa Association of Anti-Corruption Authorities.
“Ya na cewa ba su aika wa wasu ‘yan waje kudi daga cikin asusun kudin sata. Ina ganin wani kudi da aka tura a ranar 16 ga watan Afrilu, 2017." Inji Nwakocha.
KU KARANTA: Kara farashin man fetur ya zama wa Gwamnati dole - MAN
Da yake maida martani, Bawa ya ce bai dade da karbar wannan aiki ba. “Ku na sane cewa ban kai kwana 100 a ofis ba Akawun mu bai kai kwana 90 a aiki ba."
“Ba zan iya magana a kan abin da ban sani ba. Dole sai na farfado da kwakwalwata, na yi tunani.”
Bawa yace watakila dokar aiki ta ba shugaban EFCC a lokacin damar cire wadannan kudi. Nan-take shugaban kwamitin, Adejoro Adeogun ya yi masa raddi.
Hon. Adejoro Adeogun ya tambaye shi: “Ko ka na nufin wanda ka gada a kujerar ya yi amfani da wasu ka’idojin aiki, ya taba kudin da bai kamata ya taba ba?”
A nan ma dai Bawa, bai bada wata amsa ba, hakan na zuwa ne bayan an zargi hukumar da batar da wasu Naira miliyan 11 tsakanin shekarar 2017 zuwa 2018.
Asali: Legit.ng