‘Yan ta’addan Boko Haram sun jikkata mutum sama da 900 a cikin watanni 5 a 2021
- ‘Yan ta’adda sun addabi Bayin Allah a jihohin Borno, Yobe da kuma Adamawa
- Boko Haram sun kai hare-hare akalla 106 a tsakanin Junairu zuwa watan Mayu
- Sojojin Boko Haram sunyi sanadiyyar jikkatta mutum kusan 100 cikin wata biyar
Wani sabon rahoto da SBM Intelligence ta fitar, ya bayyana adadin mutanen da Boko Haram ta taba tsakanin watan Junairu zuwa watan Yunin 2021.
Jaridar The Cable ta ce alkaluman SBM Intelligence sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun kai hare-hare 106 a cikin jihohi hudu na Arewacin Najeriya.
Wannan bayani ya fito ne a wani rahoto da aka yi wa take da “After the Cat has Reached its Ninth Life, What is Next for the Boko Haram Insurgency?”
KU KARANTA: Sunayen wasu jagororin Boko Haram da Sojojin ISWAP suka damke
SBM Intelligence ta fitar da rahoton ne bayan an samu labarin dakarun Islamic State West Africa Province sun hallaka shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.
SBM ta ce wannan ne karo na bakwai da aka yi ikirarin an hallaka shugaban ‘yan ta’addan, Shekau.
‘Yan ta’addan sun fi matsawa jihohin Arewa maso gabas lamba, musamman Borno, Yobe da Adamawa, har ila yau, Boko Haram ta kai hari a Nasarawa.
Tsakanin ranar farko a shekarar nan zuwa ranar 22 ga watan Mayu, ‘yan ta’addan Boko Haram sun yi ta’adi kamar haka: Yobe 12; Borno 91, Nasarawa 2; Adamawa 1.
KU KARANTA: Ana murnar mutuwar Shekau, Hafsun sojojin kasa ya mutu a jirgi
Idan muka dauki wannan lissafi, an jikkata mutane 900 a kwanaki 143. Hakan ya na nufin fiye da mutum shida suke fuskantar barazanar ‘yan ta’addan a kullum.
Wannan ne karon farko da bangaren kungiyar Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād ta rasa shugaba tun bayan mutuwar Mohammed Yusuf da ya kafa ta.
Jaridar ta ce akwai yiwuwar wasu daga cikin sojojin Boko Haram su tattara, su bar dajin Sambisa ko su shiga kuungiyar nan ta Ansaru bayan mutuwar Shekau.
Ku na sane cewa 'yan ta’addan kungiyar Islamic State West Africa Province watau ISWAP ne su kayi sanadiyyar mutuwar Abubakar Shekau a makon da ya gabata.
Wadannan mayaka da suka shiga dajin Sambisa, sun samu horo a Libya da wasu kasashen Duniya. Shekau ya zargi mayakan da yi wa sojojinsa zagon-kasa.
Asali: Legit.ng