Gawurtaccen Attajiri, AbdulSamad Rabiu, ya ba Jami’ar Arewa gudumuwar Naira Biliyan 1
- Kamfanin BUA ya ba jami’ar UNIMAID ta garin Maiduguri gudumuwar N1bn
- AbdulSamad Rabiu Africa Initiative ta kan warewa Afrika $100m duk shekara
- Daga cikin wannan kudi ana rabawa manyan makarantun dake Najeriya $50m
Babban Attajirin ‘dan kasuwa, kuma mai kamfanin BUA Group, Alhaji AbdulSamad Rabiu, ya ba jami’ar Maiduguri, gudumuwar makudan kudi.
A ranar Litinin, 24 ga watan Mayu, 2021, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa fitaccen Attajirin ya ba jami’ar ta UNIMAID kyautar Naira Biliyan daya.
Mataimakin darektan sashen yada labarai na jami’ar tarayyar da ke garin Maiduguri, jihar Borno, Alhaji Moh’d T. Ahmed, ya bada wannan sanarwa.
KU KARANTA: Rikici na Dangote, bai son takara - BUA
Wani jawabi da aka fitar a Facebook ya nuna wadannan kudi sun shigo jami’ar ne ta hannun gidauniyar Alhaji AbdulSamad Rabiu Africa Initiative.
A baya, Darektan harkokin gwamnati wanda kuma shi ne ke kula da AbdulSamad Rabiu Africa Initiative, ASR, Dr. Idi Hong ya gana da shugaban jami’ar.
A wannan zama da aka yi a ranar Laraba da ta gabata ne Idi Hong ya sanar da Farfesa Aliyu Shugaba cewa za a ba jami’ar wannan gudumuwa mai tsoka.
Wadannan kudi suna cikin yunkurin da ake kira ASR Africa Tertiary Education grant scheme domin bunkasa manyan makarantu na gaba da sakandare.
KU KARANTA: Annobar COVID-19 ta sa kasar Saudi ta rage adadin wadanda za su yi Hajji
Da wannan kudi, jami’ar tarayyar ta Maiduguri za ta samu damar gina wani katafaren cibiyar fasaha.
Dr. Idi Hong ya yi maraba da yadda shugabannin jami’ar suka tsara za su batar da wannan kudi, ya ce hakan ya zo daidai da manufar AbdulSamad Rabiu.
Shugaban na ASR yake cewa burin Alhaji AbdulSamad Rabiu shi ne ganin mutane sun tsayu da kafafunsu don haka yake kashe $100m duk shekara a Afrika.
A watan jiya ne aka ji cewa shugaban kamfanin n BUA, Abdul-Samad Rabi'u ya bada kyautar kuɗi har Biliyan N1bn ga jami'ar Ibadan domin ayi wasu gyare-gyare.
Alhaji Rabi'u ya bada kyautar ne a wata ziyara da ya kai zuwa ofishin muƙaddashin shugaban jami'ar, Farfesa Adebola Babatunde Ekanola, a gari Ibadan, Oyo.
Asali: Legit.ng